Akume ya bayyana dalilan da suka sa aka gagara dakile matsalar 'yan bindiga
- Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da ya sa aka gagara shawo kan matsalolin kasar
- Ministan Ayyuka na Musamman ne ya bayyana dalilan a wani taro da ya gudana a Abuja
- Ya kirayi 'yan Najeriya da kowa ya bada gudunmawa wajen kawo karshen matsalolin kasar
Gwamnatin Tarayya ta ce rashin isasshen shiri na gaggawa, mayar da martani da kuma tsoma baki kan aiki ne suka haifar da babban dalilin da ya sa kasar ta zama tana fama da matsalar 'yan bindiga da sauran kalubalen rashin tsaro.
Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Sanata George Akume, ya fadi haka a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana haka ne yayin kaddamar da wani littafi mai shafi 352 mai taken: “A Planner’s Perspective on Disaster and Conflict; Issues of Forced Displacement of Persons, Management in Nigeria”, wanda Bassey Ita Etim-Ikang, wani darekta a ma'aikatar ya wallafa.
KU KARANTA: Wata sabuwa: Kabilar Yaohnanen masu bautawa mijin Sarauniyar Ingila
A cewar Akume, wanda ya kasance tsohon Gwamnan Jihar Benue, ba za a iya shawo kan matsalar ta'addanci da sauran kalubale ba tare da gudunmawar dukkan 'yan Najeriya ba.
Ya bukaci kowa ya shiga a dama da shi wajen nemo bakin zaren don warware matsalar.
"Kalubalen da ke fuskantar Najeriya sun hada da rashin isassun shiri na gaggawa da martani, da tazara tsakanin gudanar da aikin agaji da ayyukan ci gaba mai dorewa, shirin wucin gadi da kuma tsoma bakin siyasa.
"Har ila yau, akwai rashin tsarin hukumomi da na shari'a dake kula da 'yan gudun hijira a Najeriya, rashin isa ko rashin hadin gwiwar hukumomin da ke samar da mafi yawan lokuta a hukumomin da ke aiki sabanin juna tare da gudanar da ayyuka iri daya."
Ya kuma koka kan rashin ingantattun tsari tsakanin hukumomi da cibiyoyi domin tsara shirin da ya dace don ciyar da kasar gaba.
Karshe ya bayyana cewa, dukkan wani kokari bazai yi amfani matukar ba a fidda tsarin da zai yi aiki don samar da zaman lafiya da kwarin gwiwa a kasar ba.
KU KARANTA: Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya
A wani labarin, 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan gini a wani yankin jihar Ondo a ranar Talata da ta gabata.
Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin wadanda ke aikin gyara yankin Ikaram/kunnu -Akoko na kananan hukumomin Akoko ta Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Laraba, sannan ya kara da cewa an sace ma’aikatan ne a ranar Talata.
Asali: Legit.ng