APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya

APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya

- Jam’iyyar APC na ikirarin cewa Najeriya ba ta taba samun alheri a tarihinta ba har sadda Buhari ya hau mulki

- Shugaban jam'iyyar mai mulki na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Bala Buni ne yayi wannan ikirarin

- Sai dai masana tattalin arziki sun ce sama da mutane miliyan 100 a yanzu haka suna rayuwa cikin matsanancin talauci

Jam’iyya mai mulki ta APC ta yi ikirarin cewa babu wata gwamnati da ta taba yiwa Najeriya da 'ya'yanta aiki fiye da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yanzu.

Wannan ya fito ne daga mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Mai Mala Buni a ranar Talata, 20 ga Afrilu a Abuja.

Buni, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, ya yi wannan bayanin ne a wajen taron tattaunawa da manema labarai na kungiyar kwararrun jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara, sun hallaka 30 har lahira

APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya
APC ta ce ba a taba yin gwamnati mai adalci irin ta Buhari ba a tarihin Najeriya Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Buni da ya samu wakilcin sakataren kwamitin riko na jam'iyyar APC, Sanata John James Akpan Udoedehe, jaridar The Nation ta ruwaito shi yana cewa:

“Ba a yi gwamnati irin wannan ba a tarihin al’ummar kasar nan. Kuma ba ina wasa da siyasa bane. Ku nuna min wata gwamnatin da tayi abinda yafi na Shugaba Buhari da yake da alaka kai tsaye da talakawa?”

Jawabin na Buni na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugaban jam'iyyar adawa ta PDP na jihar Delta, Cif Kingsley Esiso, ya bayyana cewa jam'iyyar APC daidai take da rashin tsaro, yunwa, da talauci a kasar.

Cif Esiso ya bayyana haka ne a wurin taron nuna goyon baya ga wani dan takarar jam'iyyar PDP a zaben cike gurbi na Majalisar Dokoki na kujerar mazabar Isoko ta Arewa a jihar ta Delta.

Jam'iyyar PDP ta yi gaba ta lashe zabe a yankin kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta bayyana.

KU KARANTA: Tarihin Ibnu Battuta mai daukar hankali, daya daga cikin matafiyan da suka zagaye duniya

A wani labarin, Wani jigo a jam'iyyar APC a Zamfara, Aminu Sani-Jaji, ya ce yana maraba da Gwamna Bello Matawalle ya shigo jam'iyyarsu ta APC.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Sani-Jaji ya yi wannan bayanin ne a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Litinin, 19 ga Afrilu.

Ya bayyana cewa gwamnan na Zamfara yana da dama ta kundin tsarin mulki ya shiga kowace jam'iyyar siyasa da yake so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel