Tashin hankali: Wani mai lalurar tabin hankali ya gigita masu ibada a Masallacin Harami

Tashin hankali: Wani mai lalurar tabin hankali ya gigita masu ibada a Masallacin Harami

- Wani mai lalurar tabin hankali ya haifar da fargaba da tashin hankali a Masallacin Harami da ke garin Makka

- Mahaukacin ya yi ta fasa ihu sannan ya gigita masu gudanar da ibada tare da hana su aikinsu

- Sai dai an yi nasarar fitar da shi inda aka mika shi ga yan sandan birnin

Rahotanni sun kawo cewa hukumomi a kasar Saudiyya sun ce wani mai lalurar tabin hankali ya yi ta fasa ihu a cikin masallacin Harami da ke birnin Makka.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito daga shafin Haramain Sharifain cewa mahaukacin ya kuma hana masu gudanar da harkokin ibada yin aikinsu sannna ya yi yunkurin tashin hankali.

KU KARANTA KUMA: An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu

Tashin hankali: Wani mai lalurar tabin hankali ya gigita masu ibada a Masallacin Harami
Tashin hankali: Wani mai lalurar tabin hankali ya gigita masu ibada a Masallacin Harami Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Sai dai kuma tuni jami'an tsaro suka yi waje da mutumin daga Harami tare da mika shi ga 'yan sandan garin Makka.

A baya mun ji cewa gobara ta tashi a wasu gine-gine da ke kusa da masallacin Annabi Muhammadu (SAW) a birnin Madina da ke kasar Saudiyya, kamar yadda shafin @hsharifain ya ruwaito.

Shafin Haramain Sharifain a Twitter ya wallafa wasu hotuna da bidiyon da ke nuna wasu gine-gine na ci da wuta tare da hayaki da ya turnuke saman ginin masallacin mai daraja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu nan: Buhari ya nada mukami daga kasar Ingila, ya rubutowa ‘Yan Majalisa takarda

Ba a kuma bayyana abubuwan da suka kone sakamakon gobarar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel