Yanzu-Yanzu: Bidiyo da Hotunan Gobarar Da Ta Tashi Kusa Da Masallacin Annabi a Madina

Yanzu-Yanzu: Bidiyo da Hotunan Gobarar Da Ta Tashi Kusa Da Masallacin Annabi a Madina

- Gobara ta tashi a wasu gine-gine da ke kusa da masallacin Annabi Muhammad (SAW) a birnin Madina

- Shafin Haramain Sharifain ya ruwaito cewa an yi nasarar kashe gobarar cikin kankanin lokaci

- Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana abinda ya yi sanadin tashin gobarar ba ko abubuwan da aka rasa

Gobara ta tashi a wasu gine-gine da ke kusa da masallacin Annabi Muhammadu (SAW) a birnin Madina da ke kasar Saudiyya, kamar yadda shafin @hsharifain ya ruwaito.

Shafin Haramain Sharifain a Twitter ya wallafa wasu hotuna da bidiyon da ke nuna wasu gine-gine na ci da wuta tare da hayaki da ya turnuke saman ginin masallacin mai daraja.

DUBA WANNAN: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

Yanzu-Yanzu: Bidiyo da Hotunan Gobarar Da Ta Tashi Kusa Da Masallacin Annabi a Madina
Yanzu-Yanzu: Bidiyo da Hotunan Gobarar Da Ta Tashi Kusa Da Masallacin Annabi a Madina. Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Kawo yanzu ba a sanar da ainihin abinda ya yi sanadin tashin gobarar ba amma shafin na Haramain yace an yi nasarar kashe wutar nan take.

Ga hotunan da bidiyon a kasa:

KU KARANTA: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

Ba a kuma bayyana abubuwan da suka kone sakamakon gobarar ba.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164