Yanzu nan: Buhari ya nada mukami daga kasar Ingila, ya rubutowa ‘Yan Majalisa takarda
- Shugaban kasa ya aikawa Majalisa takardar nadin mukami da ya yi yau
- Muhammadu Buhari ya bukaci Sanatoci su tabbatar da Salisu Abdullahi
- Salisu Abdullahi shi ne mukaddashin Alkalin babban kotun da ke Abuja
Shugaban kasa ya nemi ‘yan majalisar dattawa na kasa su tabbatar da Salisu Garba Abdullahi a matsayin Alkalin babban kotun tarayya da ke Abuja.
Mai girma Muhammadu Buhari ya bukaci Sanatoci su tabbatar da Mai shari’a Salisu Garba Abdullahi a matsayin babban Alkalin kotun tarayyar.
Kafin yanzu, mai shari’a Salisu Garba Abdullahi ya na kan kujera ne a matsayin Alkalin rikon kwarya. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.
KU KARANTA: Kotu ta ce ka da a taba filayen Mahaifinsu Bukola Saraki
Dazu ne fadar shugaban kasa ta bada sanarwar wannan nadin mukami ta bakin mai magana da yawun Muhammadu Buhari watau Mista Femi Adesina.
A jawabin da Femi Adesina ya fitar, ya ce shugaban kasar ya dogara ne da sashe na 256 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wajen wannan nadin.
Adesina ya yi wa jawabin take da “Shugaban kasa ya roki majalisar dattawa ta tabbatar da Salisu Garba Abdullahi a matsayin Alkalin babban kotun Abuja.”
Adesina yake cewa wasikar ta fito daga ofishin shugaban kasar ne a ranar 1 ga watan Afrilu, 2021.
KU KARANTA: Idan Buhari ya kammala mulki, a fito da wani idaga Kudu – Gwamna
Buhari ya nemi alfarmar majalisa, ta amince da mukaddashin Alkali Salisu Garba Abdullahi, kamar yadda ta saba na’am da sauran nade-naden da ya ke yi.
Idan Garba Abdullahi ya samu amincewar ‘yan majalisar dattawan kasar, zai tashi daga Alkalin rikon-kwarya, za a rantsar da shi a matsayin cikakken Alkali.
Dazu nan ku ka samu labari cewa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari shakiyanci a kan zuwa Ingila ganin Likitoci.
Nyesom Wike ba ya goyon a kashe kudi wajen zuwa asibitocin a kasar waje. Gwamnan na Ribas ya ce ya tanadi duk abin da ake bukata a gidan gwamnatin Ribas.
Asali: Legit.ng