Ko an raba Najeriya makiyaya ba za su kasance cikin hasara ba, Miyetti Allah

Ko an raba Najeriya makiyaya ba za su kasance cikin hasara ba, Miyetti Allah

- Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana raba Najeriya da Yarbawa keson yi a matsayin alfarma ga makiyaya

- Kungiyar ta ce ba zai zama da wahala ba ga makiyaya ko da an raba kasar, domin basu rasa komai ba

- Ya kuma bayyana yadda gwamnonin arewa zasu iya sanya hannayen jari a bangaren kiwon dabbobi

Kungiyar zamantakewar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hure, ta ce makiyaya ba za su kasance cikin wahala ba idan aka raba Najeriya.

Mai magana da yawun kungiyar, Saleh Alhassan, ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake gabatarwa a wani shirin jaridar Punch wato The Roundtable.

A cewarsa, gwamnonin arewa za su bunkasa harkar kiwon dabbobi idan suka daina samun "kudin mai" daga Gwamnatin Tarayya.

Rashin jin dadin jama'a da rashin gamsuwa a kasar ya sa wasu mutane sun bayyana goyon bayansu ga kafa Kasar Yarbawa da Jamhuriyar Biafra.

KU KARANTA: Oyedepo ga Musulman Kwara: Ku bar mana makarantunmu na mishan, ba a dole

Ko an raba Najeriya makiyaya ba za su kasance cikin hasara ba, Miyetti Allah
Ko an raba Najeriya makiyaya ba za su kasance cikin hasara ba, Miyetti Allah Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Batun na Alhassan ya biyo bayan ikirarin da wasu shahararrun mutane daga yankin kudancin Najeriya ke fafutuka tare da barazanar balle yankinsu daga Najeriya.

Saboda haka, kakakin na Miyetti Allah ya ce ballewar wasu sassan kasar zai samar da dama ga arewa ta bunkasa albarkatun ta, ya kara da cewa Najeriya na fama da "tsinuwar albarkatu".

Ya kuma bayyana cewa, idan ana son gyara fasalin kasar ko kuma rabata, babu laifi, sai a zauna a teburin zagaye don tattauna yadda lamarin zai kasance.

“Shin kuna ganin idan suka raba Najeriya a yau, makiyaya zasu kasance cikin rashin nasara ne? A'a idan babu mai a cibiyoyin arewa, shin gwamnonin arewa ba za su bunkasa harkar kiwon dabbobi bane? Su wane ne masu kula da dabbobi, ba Fulani makiyaya ba ne?"

KU KARANTA: Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazu

A wani labarin daban, Hanyar Oyemekun-Oba Adesida har zuwa Alagbaka ta cika da cunkoson ababen hawa a safiyar ranar Talata yayin da jami’an tsaron Amotekun a jihar Ondo suka kai shanu 300 da aka kama zuwa hedkwatarsu.

An kame shanu sama da 100 a ranar Lahadin da ta gabata a kan babbar hanyar Akure zuwa Ilesha saboda sabawa umarnin da gwamnatin jihar ta bayar kan hana kiwo a fili da kuma kiwon makiyaya masu karancin shekaru.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.