Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazur

Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazur

- A wani bidiyo da ya shahara a kafafen sada zumunta, an ga sararin samaniyar Ka'aba ta koma ja jazur

- Lamarin da ya jawo wasu ke ganin shikenan duniyar tazo karshe, ma'ana tashin Alkashima kenan

- An bi diddgin bidiyon, an kuma gano cewa, hakan ba bakon abu bane a Massallacin na Ka'aba da sauran sassan kasar

A makon da ya gabata ne aka yi ta watsa wani bidiyo da ke nuna yadda sararin samaniyar Masallacin Ka'aba da ke kasar Saudiyya ya rikide ya zama ja jazur.

Da yawan mutane sun yi ta yada bidiyon tare da nuna yadda lamarin ya kasance, suna nuna hakan a matsayin wata alama mai nuna cewa duniya tazo karhse.

A sakon da ke yawo tare da bidiyon an ce: ... "wannan ne abin da ya faru a Saudiyya a yau, iska mai tafe da guguwar rairayin hamada mai launin ja ta rufe sararin samaniyar Masallacin Harami da kewaye."

Da ganin yadda mutane da dama da ke ci gaba da yada sakon da yin imanin cewa alamu ne na tashin Alkiyama ya sa BBC ta bi salsalar bidiyon.

KU KARANTA: Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari

Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazur
Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazur Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

An tuntubi hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Makka da Madina a kasar Saudiyya wato Haramain Sharifain ta shafinsu na Twitter, kuma sun yi bayani kan gaskiyar yadda al'amarin yake.

Haramain Sharifain ya ce irin wannan al'amari ya sha faruwa ba ma a Masallacin Ka'aba ba kawai har ma da daukacin sauran sassan kasar.

Lamarin kan faru ne a duk lokacin da iska ta taso daga Hamadar Sahara mai dauke da kura.

A duk lokacin da irin wannan iska ta taso ta kan turnuke sararin samaniyar yankunan kasar ta inda ko tafin hannu ba a iya gani.

Hukumar Haramain Sharifain ta sake cewa, a irin wadannan lokuta mutane kan dauki hotuna da bidiyo su yi ta yadawa.

KU KARANTA: Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro

A wani labarin daban, An gano wata mota kirar Mercedez Benz mallakar wani hamshakin attajiri a shekarun 1970 zuwa 1980, dan kasar Ghana mai suna Alhaji Agyaa, bayan kimanin shekaru 40 tana boye a cikin gareji.

A wani sako da shahararren dan jaridar wasanni, Saddick Adams ya wallafa a shafin Twitter, ya nuna cewa an gano motar ne a Techiman, babban birnin Techiman ta tsakiya da kuma yankin Bono ta gabas na kasar Ghana.

Wadanda suka taso a yankin sun san Alhaji Agyaa mai wadata ne kwarai, mashahuri kuma mai miliyoyin kudade da zai iya mallakar wannan Mercedes a yankin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.