Oyedepo ga Musulman Kwara: Ku bar mana makarantunmu na mishan, ba a dole

Oyedepo ga Musulman Kwara: Ku bar mana makarantunmu na mishan, ba a dole

- Wani fasto ya shawarci musulmai da su cire yaransu a makarantun mishan tunda ba dole bane

- Ya bayyana cewa, tunda ba makarantun musulmai bane, to dole su bi ka'idar makarantunsu

- Ya kuma shawarce su da su nemo makarantunsu da idan suka ga dama maza ma kan iya sanya Hijabi

Wanda ya kirkiro Cocin Living Faith da aka fi sani da Winners Chapel, Bishop David Oyedepo, ya shawarci Musulmai da su bar makarantun mishan na Kwara ga masu su.

Ya ce ya kamata su nemi makarantun da ake sanya hijabi da yaransu za su iya zuwa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a cikin watan Fabrairu ne gwamnatin jihar Kwara ta rufe makarantu 10 a kan rikicin sanya hijabi (suturar Musulunci) ta dalibai mata musulmai.

Amma a cewar rahotanni, makarantun sun ci gaba da karatu a ranar Litinin.

Da yake magana kan halin da ake ciki a wani bidiyo, Oyedepo ya ce: "Wannan mummunan al'amari ne a jihar Kwara inda Musulmai ke neman dalibansu a makarantunmu da su sanya Hijabi, alhali coci ta ce a'a.

KU KARANTA: Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazur

Oyedepo ga Musulman Kwara: Ku bar musu makarantunsu na mishan, ba a dole
Oyedepo ga Musulman Kwara: Ku bar musu makarantunsu na mishan, ba a dole Hoto: ghgossip.com
Asali: Twitter

“Ban taba ganin wani wuri a rayuwata ba inda dan haya zai ba da umarni ga maigida ba… kun san dalilin hakan? Ba mu taba nuna wa duniya wata fuskar Allah bane.

“Allah ba abin wasa ba ne. Allahnmu wuta ne mai ruruwa, bari mu nuna musu wutar Allah dake ci, suna bukatar su sani.

“Ku bar makarantun ga masu su, ku tafi makarantun ku, shin akwai wani abin fada? Ku daina tsokanar wasu.

"Coci wani bam ne mai jiran lokaci da zarar Allah ya juyo kan kowa ko wani tsarin, wannan tsarin sai ya lalace"

"Shawarata ita ce, ku bar makarantun ga masu su, ku nemo makarantunku - maza da mata za su iya sanya hijabi a can .. Ku daina sanya yatsunku a idanun wasu alhalin su ba makafi ba."

KU KARANTA: Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari

A wani labarin daban, Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi kira ga majalisar dokokin tarayya ta dakatad da wani shiri da ake yi a majalisar wakilai na yunkurin halasta amfani da Hijabi a makarantu a fadin tarayya.

A jawabin da Sakatare Janar na kungiyar CAN, Joseph Bade Daramola, ya sake, ya yi gargadin cewa wannan doka bai kamata a wannan lokaci ba, Punch ta ruwaito.

Kungiyar Kiristocin ta kara da cewa halasta sanya Hijabi zai tayar da tarzoma a Najeriya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel