'Yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu sama da 300
- A karo na biyu, 'yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu da suka haura 300 a Ondo
- A baya an kame shanu sama da 100 a kan hanyar Akure zuwa Ilesha ranar Lahadi da ta gabata
- Wannan kame na shanu ya biyo bayan umarnin hana kiwo a fili da gwamnatin jihar ta sanya
Hanyar Oyemekun-Oba Adesida har zuwa Alagbaka ta cika da cunkoson ababen hawa a safiyar ranar Talata yayin da jami’an tsaron Amotekun a jihar Ondo suka kai shanu 300 da aka kama zuwa hedkwatarsu.
An kame shanu sama da 100 a ranar Lahadin da ta gabata a kan babbar hanyar Akure zuwa Ilesha saboda sabawa umarnin da gwamnatin jihar ta bayar kan hana kiwo a fili da kuma kiwon makiyaya masu karancin shekaru.
KU KARANTA: Buhari ya karbo bashi daga waje don tallafawa masu kananan masana'antu
An ce an kame shanun 300 a kan babbar hanyar Ilesha, The Nation ta ruwaito.
Lokacin da aka tuntube shi, Kwamandan Amotekun na jihar Ondo, Cif Adetunji Adeleye, ya ce yana wurin da ake gudanar da aiki amma ya yi alkawarin zai kira daga baya.
Har yanzu bai kira ba zuwa lokacin hada wannan rahoton.
KU KARANTA: Bakuwar cuta a Kano: FG ta aika da rundunar taimakon gaggawa zuwa Kano
A wani labarin daban, Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya gargadi Sunday Igboho da wasu da ke neman kafa haramtacciyar kasar Yarbawa da su nisanci jiharsa, The Nation ta ruwaito.
Akeredolu ya ce mutanen Ondo sun zabi zama a Tarayyar Najeriya dunkulalliya kamar yadda aka tsara tun farkon kafa Najeriya.
Ya ce babu wani yanki na jihar, da aka sani kuma aka ayyana shi a matsayin jihar Ondo, da zai ba da izinin wani taro ko tashin hankali wanda zai iya ba da shawara ta kusa ko nesa, cewa mutane suna goyon bayan abin da ya kira 'rudani mai rudarwa.'
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng