Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun kashe 'yan banga sama da 20 a jihar Neja
- 'Yan banga sama da 20 sun rasa rayukansu a wani artabu da wasu 'yan ta'adda a jihar Neja
- An rahoto cewa, 'yan bindiga sun hallaka 'yan bangan tare da hana daukar gawarwakinsu
- A baya gwamnan jihar Neja ya alkawarta bai wa 'yan banga bindigogi domin yakar tsageru
‘Yan bindiga sun kashe 'yan banga sama da 20 a wani hari da suka kai Kotonkoro a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Harin kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Hausa ta ruwaito, ya faru ne a ranar Litinin bayan da 'yan banga suka yi arangama da wasu gungun 'yan bindiga a yankin.
Ibrahim Ilyasu, dan majalisar dokokin jihar daga Mariga, ya ce:
“A ranar Litinin, an yi artabu tsakanin 'yan banga da ’yan bindiga kuma suka bi su zuwa wani daji da ke kusa da su don su yake su. Abun takaici, an kashe 'yan banga kuma 'yan bindigan sun ki baiwa al'umma damar kwaso gawarwakinsu.
KU KARANTA: Matar malamin Islamiyya ta mika shi ga 'yan sanda da laifin sata a kasuwar katsina da ta kone
“Ba zan iya fadin ainihin adadin mutanen da aka kashe ba saboda sun ki ba da damar daukar gawarwakin, amma a yau (Laraba), sojoji sun je daji don kwato gawarwakin mutane 16.
"Amma wannan ba dukansu ba ne domin har yanzu akwai sauran mutanen da ba za a iya tantancewa ba saboda jikinsu ya farfashe.”
Dan majalisar ya ce an gano gawarwaki hudu a baya.
Da aka tambaye shi yadda lamarin ya faru duk da cewa ‘yan bangan na aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro, Ilyasu ya ce:
"Ba zan iya bayyana hakan ba shi ma tunda ba na nan, amma lamarin ya faru. Wadanda ke zaune a cikin al'umma na iya bayar da shaida saboda 'yan bindigan sun fatattaki wadanda suka tafi daukar gawarwakin, su (' yan bindigan) sun kusan shiga Kotonkoro.
Gwamna Abubakar Sani Bello, a cikin makonni biyu da suka gabata, ya yi alkawarin baiwa kungiyoyin 'yan banga a jihar Neja bindigogin daukar fansa, don basu damar tunkarar 'yan ta'adda da magance sauran barazanar tsaro.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansan wadanda suka sace a Abuja har N200m
A wani labarin, Wadanda suka yi garkuwa da wasu malaman makarantar firamare ta UBE a Rama da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, sun nemi a ba su Naira miliyan 15 kudin fansa kafin su saki malaman.
‘Yan bindigan a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2021, suka afkawa makarantar ta UBE suka yi awon gaba da malamai uku da yara maza uku daga wani ajin firamare, jim kadan bayan taron safe na makarantar.
Malaman makarantar daga baya sun bayyana cewa daga baya yaran uku sun tsere daga hannun 'yan bindigan.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng