'Yan bindiga da suka yi garkuwa da malamai a Birnin Gwari sun nemi N15m

'Yan bindiga da suka yi garkuwa da malamai a Birnin Gwari sun nemi N15m

- 'Yan bindigan da suka yi awon gaba da da malaman makaranta a Kaduna sun nemi kudin fansa

- Sun bayyanawa iyalan wadanda suka sacen cewa, dole ne su biya Naira miliyan 15 ga kowannensu

- An sace malaman makarantar ne wata firamaren UBE a Birnin Gwari tare da wasu dalibai da suka tsere daga baya

Wadanda suka yi garkuwa da wasu malaman makarantar firamare ta UBE a Rama da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, sun nemi a ba su Naira miliyan 15 kudin fansa kafin su saki malaman.

‘Yan bindigan a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2021, suka afkawa makarantar ta UBE suka yi awon gaba da malamai uku da yara maza uku daga wani ajin firamare, jim kadan bayan taron safe na makarantar.

KU KARANTA: Matar malamin Islamiyya ta mika shi ga 'yan sanda da laifin sata a kasuwar katsina da ta kone

'Yan bindiga da suka yi garkuwa da malamai a Birnin Gwari sun nemi N15m
'Yan bindiga da suka yi garkuwa da malamai a Birnin Gwari sun nemi N15m Hoto: mcebiscoo.com
Asali: UGC

Malaman makarantar daga baya sun bayyana cewa daga baya yaran uku sun tsere daga hannun 'yan bindigan.

Duk da haka, an tattaro daga majiyar dangin malaman da aka sace cewa 'yan bindigan sun tuntube su kuma suna neman a ba su Naira miliyan 15.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sunayen malaman da aka sace da suka hada da; Umar Hassan, Rabiu Salisu da Bala Adamu.

Da yake magana da jaridar Daily Trust, Abubakar Hussaini, wanda dan uwansa, Rabiu Salisu na daya daga cikin malaman da aka yi awwon gaba dasu, ya ce ‘yan bindigar sun nace kan biyan Naira miliyan biyar ga kowannensu kafin a sako su.

KU KARANTA: Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro

A wani labarin, Wasu tsageru dauke da makamai sun afka wa mazauna garin Kiyi a karamar hukumar Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da akalla mutane hudu.

Wani mutum Mista Salami Olalekan, memba na ma'aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCTA), an ce yana cikin wadanda aka sacen.

William Salami, dan uwan Olalekan, ya ce masu garkuwan sun nemi Naira miliyan 200, Naira miliyan 50 ga kowane wanda aka yi garkuwar da shi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel