Matar malamin Islamiyya ta mika shi ga 'yan sanda da laifin sata a kasuwar katsina da ta kone
- Wata matar malamin Islamiyya ta kai shi kara wajen 'yan sanda da zargin sace kayan jama'a
- Malamin Islamiyyan an kama shi da wasu mutane da laifin sata a kasuwar da aka yi gobara a Katsina
- Kayayyakin da aka sace sun hada da kayan masarufi da na sawa har ma da janareto a kasuwar
An kama wani mutum da aka bayyana cewa malamin Islamiyya ne dan shekara 43, cikin mutane 34 da 'yan sanda suka kwamushe a yammacin ranar Laraba kan laifin sace kayan mutane a kasuwar da iftila'in gobara ya rutsa da ita a Katsina.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa matar malamin Islmaiyyan ce ta kai shi kara wurin 'yan sanda, bayan fuskantar cewa ya wawushe kayan jama'a kuma ya boye a karkashin gado.
KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce hakan ne ya kai ga kama mutumin mai suna Muhammad Abba.
Sauran mutanen da aka kama tare da malamin kananan yara ne da suka wawushe kayayyaki irinsu kayan sawa da na amfanin gida har ma da janereto da dai sauransu.
Yanzu haka dai suna fuskantar tuhuma a wajen 'yan sandan jihar ta Katsina.
A ranar Litinin ne dai gobara ta tashi a babbar kasuwar Katsina ta yi kaca-kaca da shagunan cikin kasuwar, abin da ya kai ga tafka asarar dumbin dukiya masu darajar miliyoyin naira.
KU KARANTA: Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekaru 40
A wani labarin daban, A safiyar Litinin din nan ne gobara ta kama a babbar kasuwar Jihar Katsina, wadda aka fi sani da Central Market, rahotanni na cewa an yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a yayin lamarin.
An gano cewa wutar ta fara ne misalin karfe 8 na safe. kuma ta ci gaba da lalata shagunan da ke kasuwar, yayin da wasu da gobarar bata shafa ba ‘suka dunguma suka kwashe kayansu kafin wutar da ta tashi ta isa shagunansu.
Wakilin jaridar This Day wanda ya ziyarci kasuwar ya ruwaito cewa ba a iya gano asalin abin da ya faru da kuma yadda gobarar ta faro ba a lokacin hada wannan rahoto.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng