'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansan wadanda suka sace a Abuja har N200m
- 'Yan bindiga sun sace wasu mutane hudu a wani yankin babban birnin tarayya Abuja a Najeriya
- 'Yan bindigan sun yi awon gaba da wani jami'i sun kuma sace tukunyar gidan sun yi awon gaba
- 'Yan bindigan sun bukaci a basu kudin fansa da ya kai har Naira miliyan 200, miliyan 50 kowanne
Wasu tsageru dauke da makamai sun afka wa mazauna garin Kiyi a karamar hukumar Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da akalla mutane hudu.
Wani mutum Mista Salami Olalekan, memba na ma'aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCTA), an ce yana cikin wadanda aka sacen.
William Salami, dan uwan Olalekan, ya ce masu garkuwan sun nemi Naira miliyan 200, Naira miliyan 50 ga kowane wanda aka yi garkuwar da shi.
KU KARANTA: Zai zama wauta a kame Sunday Igboho, Mailafia ga jami'an tsaro
“Masu garkuwar sun kira sau daya, sun nemi a ba su Naira miliyan 50 kudin fansa ga mutum daya kuma lokacin da suka zo.
“Lokacin da suka afka wa gidajen, ba su dauki komai ba, sai tukunyar girki, mai yiwuwa za su yi girki ne a daji,” kamar yadda ya fada wa wakilin Daily Trust ta wayar.
Sauran ukun da lamarin ya rutsa da su sun hada da matukin babur, makanike da kuma direban tasi.
An gano cewa ’yan bindigan sun shiga gidan Olalekan ta tagar baya. An ce sun lalata sandunan karfe na tagar kafin su sami shiga cikin gidan nasa.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na FCT, ASP Miriam Yusuf, ta ce,“Mun fara gudanar da aiki don ceto wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma cafke wadanda ake zargin da suka tseren.”
KU KARANTA: Tsoron kada a bincikeshi, wani attajiri ya boye motarsa tsawon shekaru 40
A wani labarin, Sojojin Kamaru biyu da aka tura zuwa Najeriya sun mutu da yammacin ranar Asabar a wani harin Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, in ji majiyar sojojin Najeriya a ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.
Masu tayar da kayar bayan, tafe a kafa da kuma a cikin manyan motocin da ke dauke da muggan makamai, sun afka wa sojojin Najeriya a wajen garin Wulgo. Hakanan an kaiwa sojojin Kamaru hari bayan girke su daga ketaren iyaka don taimakawa rundunar.
"Sojojin CDF (Dakarun Tsaron Kamaru) biyu sun mutu a musayar wuta na tsawon minti 40 tare da 'yan ta'addan Boko Haram," in ji majiyar sojojin Najeriya.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng