Da dumi-dumi: Wasu daliban firamare da aka sace a Kaduna sun tsere daga hannun 'yan bindiga

Da dumi-dumi: Wasu daliban firamare da aka sace a Kaduna sun tsere daga hannun 'yan bindiga

- Wasu dalibai uku da aka sace a safiyar yau Litinin sun tsere daga hannun 'yan bindiga

- Wata malamar makarantar ta tabbatar da kubutar daliban, sai dai babu labarin malamansu

- Biyo bayan satar, kwamishinan tsaro na jihar ya tabbatar da faruwar lamarin a makarantar

Wasu daliban makarantar firamare uku da aka sace ‘yan awanni da suka gabata lokacin da wasu 'yan bindiga suka farma makarantar firamaren UBE da ke Rama a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun tsere.

Da yake zantawa da daya daga cikin malaman makarantar, Daily Trust ta tattaro cewa tun farko an sace dalibai uku na firamare amma sun tsere lokacin da ‘yan bindigar suka yi kokarin satar wasu shanu da babura a wata unguwa da ke kusa.

Naomi Francis, wata malama a makarantar, wacce ta tsira daga satar, ta tabbatar wa Daily Trust cewa daliban uku sun kubuta amma ta ce 'yan bindigan sun buge su.

Sai dai, babu wani labari game da malamai ukun da aka sace tare da daliban.

Da take bayanin yadda ‘yan bindigan suka kutsa kai cikin makarantar, ta ce: “Sun shigo ne bayan taron da safe (na makarantar).

KU KARANTA: Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3

Da dumi-dumi: Wasu daliban firamare da aka sace a Kaduna sun tsare daga hannun 'yan bindiga
Da dumi-dumi: Wasu daliban firamare da aka sace a Kaduna sun tsare daga hannun 'yan bindiga Hoto: The Nation
Asali: UGC

“Dukkanmu mun shiga ajujuwa ne a lokacin da 'yan bindigan su shida suka zo kan babura yayin da wasu suka kewaye makarantar.

“Na fita daga aji na lokacin da na lura daliban ajin firamare na 5 da 6 sun gudu.

"Nan da nan na sanar da dalibaina su gudu kuma sun yi."

Shima da yake magana, wani mazaunin garin Mai Saje Rama, ya tabbatar da cewa daliban sun dawo cikin garin amma ya ce ba a san inda malaman suke ba.

"'Yan banga da suka bi su sun dawo ba tare da nasara ba, ba su iya gano 'yan bindigan ba," in ji shi.

Kansilan Rama, Aliyu Isa ya fada tun farko cewa babu wani dalibi da aka sace.

Ya yi ikirarin cewa 'yan ta'addan sun kai hari ne a wani kauye da ke kusa da su sannan suka yi awon gaba da mutum biyu tare da sace wasu shanu.

Kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, bai amsa kiran da aka yi masa ba kuma an tura sakon tes a wayar sa bai amsa ba.

KU KARANTA: Indiya za ta bi sahun Najeriya a harmata Bitcoin tare da garkame masu shi

A wani labarin, Yan bindigan da suka sace daliban makarantar FCFM Afaka a jihar Kaduna sun bukaci N500m daga wajen gwamnatin jihar domin fansan dalibai 39 - Mata 23 da Maza 16.

Daily Trust ta rahoto cewa akalla iyayen uku cikin daliban sun tabbatar da cewa yan bindigan sun tuntubesu kuma sun bukaci N500m kafin su sakesu. Hakazalika yan bindigan sun saki bidiyoyi uku na daliban da suka sace cikin daji.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.