Jihar Katsina ta gurfanar da Dr Mahadi Shehu a gaban kotu da zargin batanci

Jihar Katsina ta gurfanar da Dr Mahadi Shehu a gaban kotu da zargin batanci

- Mai kwarmato bayanan sirri a jihar Katsina ya gurfana a gaban kotu tarayya dake jihar ta Katsina

- Ana Zargin mutumin da aikata laifin watsa bayanan batanci game da gwamnatin jihar ta Katsina

- Kwamishinan shari'a na jihar ya tabbatar da cewa, kalaman da yake watsawa na karya ne

Mai kwarmato bayanan sirri a jihar Katsina, Mahadi Shehu ya isa Babbar Kotun Tarayya da ke jihar don fara sauraron karar da ake zargin Gwamnatin Jihar da yi masa na aikata laifuka ta yanar gizo.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa a ranar 4 ga Fabrairu, 2021, Gwamnatin Jihar Katsina ta gurfanar da Shehu a gaban kotu a bayan da Kwamishinan Shari’a na Jihar kuma Babban Mai Shari’a na Kasa, Ahmad El-Marzuq ya shigar da kara a gaban kotu.

KU KARANTA: Rudani yayin da sojoji suka gano kayan sojoji, katin shaida na sojoji 145 a Borno

Jihar Katsina ta gurfanar da mai kwarmato bayanan sirri Mahadi Shehu a gaban kotu
Jihar Katsina ta gurfanar da mai kwarmato bayanan sirri Mahadi Shehu a gaban kotu Hoto: Katsina Beat
Asali: UGC

A cewar El-Marzuq, gwamnatin jihar ba ta da wani zabi face ta gurfanar da mutumin a gaban kotu bayan bin tsarin da ya dace, yana zargin cewa wanda ake tuhumar ya bayyana a wasu dandalin sada zumunta yana yin zarge-zargen wuce gona da iri kan gwamnatin jihar.

Dukkanin bayanan da Mahadi ya wallafa a shafukan sada zumunta a cewar El_Marzuq da aka samu na bogi ne kuma cike suke da karya.

Kwamishinan ya yi zargin cewa bayan sakin Mahadi a kan beli sai ya tsallake belin ya buya, yana mai bayyana cewa mutumin da ake magana da shi ya kai rahoto ga ’yan sanda biyo bayan bukatun gwamnatin jihar inda aka kama shi kuma aka ba da belinsa.

Don haka, ana sa ran alkalin kotun, Mai Shari'a Hadiza Shagari za ta fara sauraren karar ta farko.

KU KARANTA: Tsohon shugabab kwalejin ilimi (FCE) ta Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu

A wani labarin, Dan siyasa kuma mai kafar yada labarai ta yanar gizo, Sahara Reporters, Omoyele Sowore, an yi masa rakiya zuwa Kotun Majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja, a ranar Talata tare da wani mutum sanye da riga mai launin ja da baki mai tsayo zuwa gwiwa da hularta

Mutumin, wanda bai bayyana sunansa ba, yana daga cikin magoya bayan Sowore da ke kotun don shaida yadda ake gudanar da shari’arsa, tare da wasu mutum hudu, kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, hada taro ba bisa doka ba da kuma tunzura jama’a.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel