Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba

Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba

- Sowore ya bayyana a gaban kotu da wani bakon al'amari da ba saba gani ba a yankin

- Ya bayyana ne tare da wani mutumin da yafi kama da mai duba a fina-finan Ibo a Najeriya

- A yayin zaman shari'ar, an dage masa takunkumin hanashi barin birnin Abuja zuwa wata jiha

Dan siyasa kuma mai kafar yada labarai ta yanar gizo, Sahara Reporters, Omoyele Sowore, an yi masa rakiya zuwa Kotun Majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja, a ranar Talata tare da wani mutum sanye da riga mai launin ja da baki mai tsayo zuwa gwiwa da hularta

Mutumin, wanda bai bayyana sunansa ba, yana daga cikin magoya bayan Sowore da ke kotun don shaida yadda ake gudanar da shari’arsa, tare da wasu mutum hudu, kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, hada taro ba bisa doka ba da kuma tunzura jama’a.

An bayyana mutumin a matsayin bokan Sowore, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba
Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba Hoto: The Nation
Asali: UGC

Rigar sa tana dauke da wani kayan ado da bawon katantanwa da karamin kan dila da akayi zane akai.

Yana dauke da sanda da karamar wutsiyar shanu rike a hannun damansa; Yana kuma rataye da jan buhu mai zane a kafadarsa.

Mutumin yana da alamun alli kewaye da idanunsa kuma bai sanya takalmi ba.

Bayyanar sa a bakin kotun ya haifar da kallo tsakanin mutane a kewayen harabar kotun.

Kamar sauran wadanda suke tare da Sowore, mutumin, wanda ya yi kama da mai duba a fina-finan Ibo, an ba shi izinin shiga kotun.

A yayin shari'ar, wani mai gabatar da kara, jami'in 'yan sanda, ya ba da shaida game da yadda aka kama wadanda ake tuhumar da sanyin safiyar 1 ga Janairun 2021 yayin da ake zarginsu da yin taro ba bisa ka'ida ba da tayar da hankalin jama'a.

Shaidan ya ce, rundunar ‘yan sanda ce ta cafke wadanda ake zargin a mahadar Lokogoma da ke Abuja.

Yayin da lauyan da ke amsa tambayoyin wadanda ake tuhumar, Marshal Abubakar, mai shaida ya ce shi da kansa bai kama Sowore ba, amma shi memba ne na tawagar da ta yi nasarar cafke dukkan wadanda ake tuhumar.

Kafin dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 7 ga Mayu na wannan shekarar, Alkalin ta banbanta sharuddan da aka gindaya a kan belin da aka ba wadanda ake tuhuma na biyu zuwa na biyar ta hanyar ba su izinin yin tafiya zuwa wajen Abuja.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo

A wani labarin, Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da Sanata Umaru Tafida-Argungu a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato kan tuhuma daya da ake yi masa na karkatar da kudin jama’a har N419,744,612.30.

A wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce tsohon sanatan wanda ya wakilci Kebbi ta Arewa a majalisar dattijai ya karkatar da adadin da gwamnatin jihar Sakkwato ta biya a matsayin 40% na hannun jari a Hijrah Investment Nigeria Limited.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel