Rudani yayin da sojoji suka gano kayan sojoji, katin shaida na sojoji 145 a Borno

Rudani yayin da sojoji suka gano kayan sojoji, katin shaida na sojoji 145 a Borno

- Rundunar sojoji a jihar Borno ta gano kakin sojoji da sauran kayan aiki soji na mutum 145

- Rundunar ta shiga rudani da ganin kayan biyo bayan sauyin wurin aiki da aka yi wa sojojin

- Wasu da lamarin ya rutsa dasu, sun ce kwamandansu ne ya kwaci kayayyakinsu basu san kuma matsayinsu ba

An samu rudani lokacin da jami'an runduna ta 7 ta sojojin Najeriya dake Maiduguri, suka gano kakin sojoji da katunan shaidar sojoji 145 da aka sauya a garin Marte da ke jihar Borno.

Lamarin ya faru ne ‘yan awanni kadan bayan da aka binne sojoji bakwai da aka kashe a wata arangama da suka yi da masu tayar da kayar baya a ranar 14 ga Fabrairu, 2021

A yayin harin, rahotanni sun ce maharan sun kona kayayyakin soji, da suka hada da motoci, tare da sace babura da kayayyakin abinci.

KU KARANTA: Watakila mace ta gaji kujerar shugaba Buhari a zaben 2023, Zainab Marwa

Rudani yayin da sojoji suka gano kayan sojoji, katin shaida na sojoji 145 a Borno
Rudani yayin da sojoji suka gano kayan sojoji, katin shaida na sojoji 145 a Borno Hoto: The Punch
Asali: Twitter

A makon da ya gabata, an tura sojoji, wadanda ke aiki tare da Bataliyar 153 ta Task Force a Marte, tun a shekarar 2017, zuwa Maiduguri yayin da aka yi amfani da wadanda suka fito daga sansanin soja na Jaji a jihar Kaduna don maye gurbinsu.

Amma hukumomin sojojin sun gano kakin sojoji, katin shaida da duk wasu kayayyakin aiki daga sojojin wadanda a da suke Marte.

Daya daga cikin sojojin da abin ya shafa ya ce duk da cewa babu wani tabbaci a hukumance daga hukumomin tsaro kan ko an sallame su daga aiki,

“Babban Kwamandanmu ya kawo karshen aikin da muke yi bayan karbar kakin sojanmu da katin shaida. Yawancinmu mun tafi gida yayin da wasunmu da ke cikin rudani game da lamarin suke jiran tsammani.”

Wata majiyar ta ce an nemi sojojin da abin ya shafa su ci gaba da hutu na kwanaki 90.

Lokacin da aka tuntubi Daraktan Hulda da Jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed M.Yerima, ya ce har yanzu sojojin da abin ya shafa suna cikin aikin sojojin.

KU KARANTA: Yahaya Bello zai magance matsalar tsaro a Najeriya kamar yadda ya yi Kogi idan...

A wani labarin, Jami'an tsaro a Kaduna sun tabbatar da kashe akalla 'yan bindiga hudu a wani kwanton bauna da aka yi a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An kwato bindigogi uku da gatari daya daga hannun 'yan bindigar, wadanda suka kasance 'yan kungiyar ta'addancin da ke addabar sassan jihar. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da kisan 'yan bindigan.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel