Gwamnan jihar Gombe ya rantsar da dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina

Gwamnan jihar Gombe ya rantsar da dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina

- Gwamnan jihar Gombe ya nada dan marigayi Mai Tangale Abdu Buba Maisheru na Billiri

- A makon nan ne gwamnan jihar yayi waje da wasu kwamishinoninsa ya kuma nada sabbi

- Gwamnan ya kuma bayyana nada sabbin kwamishinonin da inganta ci gaban jihar ta Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya rantsar da babban dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina, Daily Trust ta ruwaito.

Christopher Abdu Maisheru, dan marigayi sarkin, an rantsar dashi tare da Idris Abdullahi Kwami da Abubakar Aminu Musa, bayan tantancewa da tabbatarwa da su da majalisar dokokin jihar Gombe tayi.

An tura Maisheru zuwa Ma’aikatar Ayyuka na Musamman; Idris Kwami ya kasance a ma’aikatar gidaje da ci gaban birane, yayin da Musa aka tura shi ma’aikatar ci gaban matasa.

Gwamnan ya riga ya kori tsoffin kwamishinonin lafiya, Dr Ahmed Gana, Alhassan Kwami (kwamishinina Bayanai da Al'adu) da Mela Nunghe (kwamishinan Ayyuka na Musamman).

KU KARANTA: Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji kan mutane

Gwamnan jihar Gombe ya rantsar da dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina
Gwamnan jihar Gombe ya rantsar da dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina Hoto: The Guardian
Asali: UGC

A nasa jawabin, Gwamna Yahaya ya ce sabbin nade-naden sun dogara ne da tarihin aiki, sadaukar da kai ga aiki da kuma kyakkyawar gudummawa don ci gaban jihar.

Don haka, ya bukaci wadanda aka nada su yi aiki ba tare da gajiyawa ba da nufin tabbatar da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata.

Gwamnan ya kuma yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da marawa gwamnatinsa baya, “a ci gaba da kokarinta na samar da ababen more rayuwa da tattalin arziki don inganta jin dadin mutanenmu.”

Da yake mayar da martani a madadin takwarorinsa, Idris Kwami, ya yaba wa gwamnan kan gano su da yayi da dacewar nada su a matsayin mambobin majalisar zartarwar jihar.

Ya yi alkawarin yin biyayya ga gwamnati sannan ya ba da tabbacin yin aiki tukuru tare da tabbatar da amincewar da gwamnan ya yi masu.

KU KARANTA: EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

A wani labarin, Gwamnan Gombe Muhammadu Yahaya ya nada sabon Mai Tangale, Daily Trust ta ruwaito. An bayyana nadin Danladi Sanusi Maiyamba a ranar Laraba.

Ana sa ran za a kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan kan sarautar gargajiya ta Mai Tangale a garin Billiri dake Gombe.

Kwamishina, a Ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin Masarauta, Ibrahim Jalo ya isar da amincewar Gwamnan kuma ya gabatar da nadin daga baya ga sabon Mai Tangle a Poshiya dake Billiri.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel