Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji kan mutane

Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji kan mutane

- Wasu jami'o'i a Najeriya sun yi kokarin samar da allurar rigakafin COVID-19 a wani bincike

- Masanan da suka gudanar da binciken hada kai ne wajen gudanar da wannan babban aiki

- A hain yanzu, ana ci gaba da gwajin rigakafin a kan dabbobi kafin a zoga kan halittar dan Adam

Shugaban jami’ar Adeleke, Farfesa Solomon Adebiola, ya bayyana cewa riga-kafin kwayar cutar COVID-19 da masana kimiyya na Najeriya suka kirkiro a halin yanzu tana matakin gwaji na asibiti, Vanguard News ta ruwaito.

Ya kara da cewa allurar, wacce Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita kuma ta sami goyon bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta samu ne daga wani masanin kimiyya daga Jami’ar Adeleke, Dokta Oladipo Kolawole, tare da hadin gwiwar wasu daga wasu jami’o’i biyar na kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai a majalisar dattijai ta jami’ar a bikin cikar makarantar shekaru goma, Farfesa Adebola ya ce allurar rigakafin na daya daga cikin biyu daga Afirka kuma ita kadai ce daga Najeriya, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) ta amince da ita.

“A yanzu haka, allurar rigakafin tana matakin gwaji na asibiti, inda muke gwaji kan dabbobi kafin ta koma gwaji kan dan adam.

KU KARANTA: EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji
Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji Hoto: CNN
Asali: UGC

"Masanin kimiyyar da ke jagorantar binciken ya fito ne daga Jami’ar Adeleke, Dakta Oladipo Kolawole, tare da hadin gwiwar masana kimiyya daga sauran jami’o’i."

A jawabin ya bayyana jami'o'in "wadanda suka hada da Precious Cornerstone, Jami’ar Ilorin, Jami'ar Ladoke Akintola dake Ogbomoso, Jami'ar Obafemi Awolowo da Jami'ar Elizade”.

Mataimakin Kodinetan tawagar, Farfesa Olubukola Oyawoye ya ce allurar rigakafin ta cika ka’idar kasa da kasa, inda ya kara da cewa an yi aikin raba sinadarin ‘ribonucleic acid’ na allurar a wani dakin binciken kwayoyi na Amurka.

Da yake magana kan nasarorin da jami’ar ta samu a cikin shekaru goma, Shugaban Jami’ar ya ce ya yaye dalibai 1863 tun daga shekarar 2015 yayin da kwasa-kwasai 30 da take da su a dukkanin fannoni shida na jami'ar aka amince da su a gwamnatance.

Jami'ar da ta fara karatu a ranar 30 ga Oktoba shekarar 2011, a cewar Farfesa Adebola ta mai da hankali ne karantarwa a kwalejin likitanci na magunguna, harhada magunguna, ilimin magunguna, likitancin kashi a shirinta na bunkasuwa karo na biyu.

“Cutar nan ta Covid-19 wacce ta kawo tabarbarewar ayyukan ilimi a Najeriya da sauran sassan duniya ta fitar da wasu dabaru daga cikin mu.

“Tare da taimakon fasahar bayanai da sadarwa, jami’ar ta sauya zuwa koyarwa ta yanar gizo…

"A bisa wannan nasarar, Jami’ar ta zabi cewa za a gudanar da koyarwa da jarabawa ga Kwalejin Ilimi na Gaba daya ta yanar gizo kuma za a fadada shi zuwa wasu fannonin zuwa wani lokaci”, ya kara da cewa.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnati ta amince da biyan N797.2bn na aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano

A wani labarin, Allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca da NAFDAC ta amince dasu sun iso kasar Najeriya da tsakar ranar Talata, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta wani kamfanin jirgin sama na Emirates, Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban kwamitin tsaro na shugaban kasa (PTF) kan COVID-19, Boss Mustapha, ya fada a ranar Asabar cewa Najeriya za ta karbi kaso na farko na kimanin allurai miliyan 4 na COVID-19.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therlee

Asali: Legit.ng

Online view pixel