EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

- Hukumar EFCC ta bukaci 'yan Najeriya da su dakata da taya shugabansu murna a wannan lokacin

- Hukumar ta kula cewa, ana zubar da kudade ne kawai wajen taya shugaban na EFCC mrna

- Hakazalika hukumar ta bayyana ba murna yake bukata ba; yafi bukatar a taya shi addu'a bashi goyon baya

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bukaci masu yi wa sabon shugaban da aka nada, Abdulrasheed Bawa, fatan alheri da su daina biyan kudi don taya shi murna, The Nation ta ruwaito.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ta Wilson Uwujaren ya fitar a shafin Twitter @OfficialEFCC, EFCC ta ce dukiyar da aka kashe kan sakonnin taya murnar za a iya kaiwa ga yin abubuwan da suka dace, kamar tallafawa 'yan gudun hijira.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo

EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaba
EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaba Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Hukumar ta EFCC ta ce ta lura da yawan sakonnin da kungiyoyi da daidaikun mutane ke fitarwa a kafafen yada labarai, suna taya Bawa murnar nadin, amma ta lura cewa shugaban na bukatar goyon baya da addu’a ne kawai ba murna ba.

"Yayin da bude baje kolin nuna kauna da goyon baya na iya zama abin yabo a al'adurmu, kuma hakika an yaba da hakan, amma duk da haka ba shi da amfani a wannan lokacin kuma a hankali ya zama wani abu mai dauke hankali," in ji sanarwar.

“Mr. Bawa yana karbar shugabancin EFCC a lokacin da yake fuskantar babban kalubale kuma yana son tsayawa da kafafunsa.

"Abin da yake bukata daga masu yi masa fatan alheri da kuma dukkan 'yan Najeriya, shi ne goyon baya da addu'o'i, kuma mafi mahimmanci, sahihan bayanan da za su kawo ci gaba ga aikin Hukumar," in ji Hukumar

KU KARANTA: Da alamu gwamnatin Buhari bata fahimci matsalar tsaro a Zamfara ba, in ji gwamna Matawalle

A wani labarin, Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da Sanata Umaru Tafida-Argungu a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato kan tuhuma daya da ake yi masa na karkatar da kudin jama’a har N419,744,612.30.

A wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce tsohon sanatan wanda ya wakilci Kebbi ta Arewa a majalisar dattijai ya karkatar da adadin da gwamnatin jihar Sakkwato ta biya a matsayin 40% na hannun jari a Hijrah Investment Nigeria Limited.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel