Kungiyar Kwadugo NLC ta Shirya Zanga Zanga akan Shirin Yan Majalisu Na Chanja Mafi Karancin Albashi

Kungiyar Kwadugo NLC ta Shirya Zanga Zanga akan Shirin Yan Majalisu Na Chanja Mafi Karancin Albashi

- Zamuyi zanga zanga akan shirin yan majalisu na chanja ma mafi karancin albashi tsari, cewar yan kwadago

- Idan bukatar yajin aiki ta taso to zamu tsunduma baji ba gani

- Ayuba Waba shugaban Kungiyar ya bayyana haka bayan wani taron gaggawa a Abuja

Kungiyar kwadugo ta kasa NLC tace zata fara zanga zangar Lumana a ranar 10 ga watan Maris, 2020 bisa shirin da yan majalisu keyi na chanja tsarin mafi karancin albashi daga inda yake a yanzun.

Kamar Yadda Punch ta wallafa, Kungiyar tace, Zanga zangar zata gudana a dukkan Majalisun dokoki na jihohi 36 domin nuna rashin amincewar su akan shirin yan majlisun tarayya na chanja tsarin mafi karancin albashi, wanda yaba gwamnatin tarayya damar shiga fagen tattaunawa da ma'aikata akan mafi karancin albashi na kasa.

A wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki na kungiyar suka gudanar ranar Talata a Abuja, shugaban kungiyar, Ayuba Wabba, ya sha alwashin Kungiyar bazata yarda da duk wani shiri na wargaza tsarin aikin kasar nan ba.

KARANTA ANAN: Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a Jihar nija

A makon da ya gabata, majalisar wakilai ta kasa ta gabatar da wani kuduri na cire damar tattaunawa akan albashi daga "Ecxlusive" zuwa "concurrent list" wanda ka iya sa gwamnonin kasar nan su gaza biyan mafi karancin albashi N30,000 akan sabon tsarin.

Kungiyar Kwadugo NLC Ta Shirya Zanga Zanga Akan Shirin Yan Majalisu Na Chanja Mafi Karancin Albashi
Kungiyar Kwadugo NLC Ta Shirya Zanga Zanga Akan Shirin Yan Majalisu Na Chanja Mafi Karancin Albashi
Asali: Facebook

KARANTA ANAN: Afenifere, Igboho da OPC sun shirya gangamin hannun riga da naman shanu

A lokacin da yake karin haske akan shirin zanga zangar, Wabba yace ba zai yuwu Ma'aikata su zauna suna kallon wahalar da suka sha don kwato yancinsu ta salwanta ba ta hanyar wasu yan siyasa masu karancin tunani.

A wata sanarwa da shugaban kwadugo da sakataren rikon kwarya, Isma'il Bello suka rattafa hannu, sun kira kudurin da "Kokarin rushe ma'aikatun Nigeria".

Ya ce "Majlisar zartarwar kungiyar ta yanke fara gudanar da zanga zangar lumana ranar 10 ga watan maris a babban birnin kasar musamman majalisar wakilai"

"Sun kuma yanke cewa idan bukata ta taso, zasu bawa masu zartar da kungiyar na kasa damar shiga yajin aiki a Kasa baki daya, matukar yan majilisun suka cigaba da kudurinsu na chanja mafi karancin alabashi daga "Exclusive 'legislative list' zuwa 'Concurrent legislative list'.

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ribas ya sasanta gwamnonin johohin Benue da Bauchi kan rikicin makiyaya

Gwamnan Benue Samuel Ortom da takwaransa na jihar Bauchi Bala Mohammed a ranar Talata sun rungumi juna bayan sulhun da to Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya shirya, The Nation ta ruwaito.

Gwamnonin biyu sun yi rikici a bainar jama'a game da kashe- kashen makiyaya a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel