Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a jihar Neja

Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a jihar Neja

- Hukumar ta NDLEA ta cafke wasu kungiyar mutane biyu na dillalan bindigogi a jihar Neja

- Wadanda ake zargin sun kasance dauke da AK-47 guda 12 da kuma bindiga kirar gida guda 15

- Rahotanni daga hukumar sun ce an cafke tawagar ne a ranar Litinin, 1 ga watan Maris

Koda dai gwamnatin Neja ba ta fitar da sanarwa a hukumance da ke sanar da cafke masu satar mutanen da suka sace daliban Kagara ba, amma hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta damke wasu bindigogi daga hannun miyagu a jihar.

A cewar shugaban rundunar ta NDLEA a Neja, Aloye Isaac Oludare, an kama wadanda ake zargin, Danjuma Auta da Daniel Danrang a ranar Litinin, 1 ga Maris, kan hanyar Kontagora-Zuru, TVC News ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ba yaki ake yi a Najeriya ba, ACF ta bukaci kungiya da ta janye takunkumin abinci kan kudu

Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a jihar Neja
Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a jihar Neja Hoto: TVC News
Asali: UGC

Oludare ya bayyana cewa an kama dillalan bindigogin ne da bindigogin AK 47 guda 12 da kuma kananan bindigogi guda 15.

Shugaban hukumar ta NDLEA a Neja ya ce, su biyun sun boye makaman ne a cikin buhu kuma suna kokarin kai su wani boyayyen wuri lokacin da aka kama su.

Ya ce: “Kontagora inda aka kame makaman yana da nisan kilomita 107 daga Kagara, wani gari a Jihar Neja inda aka yi garkuwa da mata da yara da daliban makarantar sakandare a cikin wata daya da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Kada kubari a yaudare ku, Gwamnan Bauchi yayi kira ga al'ummar Mazabar Dogara

"Binciken farko ya nuna cewa wanda ya kirkiri makaman yana zaune ne a Kamfaninwaya, wanda ba shi da nisa da Kontagora, yayin da daya daga cikin kananan bindigogin ke dauke da harsasai."

A wani labari, Hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyii a Najeriya ta karbe kwayoyi na sama da Naira biliyan 60 a fadin Najeriya a makonni shida.

A ranar Litinin, 1 ga watan Maris, 2021, NDLEA ta bayyana cewa ta ci wannan nasara ne bayan Janar Mohamed Buba Marwa ya zama shugabanta.

Janar Mohamed Buba Marwa (rtd) ya yi kira ga shugabannin addini su bada gudumuwa wajen yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a kasar nan.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel