Afenifere, Igboho da OPC sun shirya gangamin hannun riga da naman shanu

Afenifere, Igboho da OPC sun shirya gangamin hannun riga da naman shanu

-Dillalan dake daukar shanu da kayan abinci daga arewa zuwa kudu sun kauracewa yankin domin nuna rashin jin dadinsu akan kisan da ake ma 'ya'yanta

- Kwana hudu kenan da fara yajin aikin masu safarar shanu wanda hakan ya jawo tashin gwauron zabi na shanu a kudancin kasar

- AUFCDN tayi kira ga gwamnatin kasar da ta biya diyyar rayukan da aka rasa

Kungiyar kare hakkin Yarbawa ta Afenifere, tare da Gani Adams, Sunday Adeyemo wanda akewa lakabi da Igboho da kuma Mutanen Odua karkashin jagorancin yarima Segun Osinbote sun shirya tsaf domin kaddamar da shirin nuna kyamar amfani da naman shanu.

Shirin wanda suka yiwa lakabi da "Anything, But Cow Day" za'a kaddamar dashi a ranar Jumua, 5 ga watan Maris din da muke ciki 2020. An shirya hakan ne biyo bayan kauracewar da yan kasuwar arewa sukayi wa kudancin kasar. A yau dai kauracewar ta shiga rana ta 4.

Shirin wanda akayi ma take da "End COWVID-21" ana tsammanin zai jawo hankalin mutane dayawa musamman a manhajar Twitter da "#endcowpandemic" kuma za'a nuna shi kai tsaye a wata tasha ta YouTube mai suna Odua Peoples Communications Youtube channel.

A halin yanzu dai, Yajin aikin da masu dillancin shanu da kayan abinci suka fara karkashin hadakar kungiyoyin masu dillancin Shanu da kayan abinci na kasa (AUFCDN) ya shiga kwana na 4.

Yajin aikin wanda ya kunshi kulle duk wata hanyar da za'a iya kai kaya data hada Arewacin kasar da Kudanci ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

A wani taro da tayi ranar Litinin a Abuja, AUFCDN tace, an gayyaci shuwagabannin ta zuwa wani hukumar DSS akan hana safarar kayan abinci da kuma shanu daga arewaci zuwa kudancin kasar.

Sakataren AUFCDN , Ahmed Alaramma, ya kara da cewa a yanzu haka shugaban kungiyar na tare da Jami'an tsaro na farin kaya DSS.

DUBA NAN: Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya

Yarabawa Zasu Shirya Gangamin Nuna Kin Jinin Naman Shanu
Yarabawa Zasu Shirya Gangamin Nuna Kin Jinin Naman Shanu
Asali: UGC

DUBA NAN: Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro

A bangare guda, wasu manoman albasa da ‘yan kasuwarta a jihar Kano suna kukan kan tasirin katange kai kayan abinci zuwa yankin kudancin kasar nan.

Yayinda farashin kayayyakin masarufi ya hauhawa a kudu, a arewa farashin na ta faduwa warwas.

A ranar Talata, Daily Trust ta ziyarci Kasuwar Albasa ta Gun-Dutse da ke karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano don ganin yadda ’yan kasuwar ke jure zafin yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel