Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya

Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya

- Gwamnan jihar Ribas ya sasanta gwamnonin johohin Benue da Bauchi kan rikicin makiyaya

- Gwamnonin biyu sun kasance suna caccakar juna dangane da wani sabanin ra'ayi na yanki

- Gwamnonin biyu sun rungumi juna bayan tattaunawa da gwamnan jihar Ribas da na Adamawa

Gwamnan Benue Samuel Ortom da takwaransa na jihar Bauchi Bala Mohammed a ranar Talata sun rungumi juna bayan sulhun da Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya shirya, The Nation ta ruwaito.

Gwamnonin biyu sun yi rikici a bainar jama'a game da kashe-kashen makiyaya a fadin kasar.

Bala Mohammed ya kare makiyaya kan daukar bindigogin AK-47, yana mai cewa suna yin hakan ne domin kare kansu.

KU KARANTA: Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro

Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya
Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Shi kuwa Ortom ya caccaki Gwamnan Bauchi bisa zarginsa da goyon bayan aikata laifuka tare da yi masa lakabi da "gwamnan ta'addanci".

An yi sulhu mai nuna alamar an cimma matsaya bayan taron a gidan Wike na musamman a Fatakwal tare da Ortom da Mohammed inda suka rungumi juna.

KU KARANTA: Atiku ya gargadi Buhari: Kada ka yarda a sake sace dalibai a kasar nan

A wani labarin, Gwamnatin jihar Benue ta saki shanu 210 da masu gadin dabbobi a jihar suka kwace a Mbala dake fadar jihar a Makurdi, da Gbajimba a karamar hukumar Guma duk a jihar, Channels Tv ta ruwaito.

An mayar da shanun ga masu su bayan an biya tarar daban-daban na kimanin Naira miliyan 5.

Kwamandan masu kula da kiwo na jihar Benue, Linus Zaki, yayin da yake mayar da shanun ga masu su, ya gargade su da su guji karya dokar hana kiwo a fili ta shekarar 2017 tare da neman amincewa don kafa wuraren kiwo.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.