Miyetti Allah ta na yi wa Yarbawa horo da yunwa, ba za a kai abinci ba sai an kare rayukan Fulani

Miyetti Allah ta na yi wa Yarbawa horo da yunwa, ba za a kai abinci ba sai an kare rayukan Fulani

- Kungiyar Miyetti Allah ta ce za a cigaba da hana kai wa ‘Yan kudu abinci

- MACBAN ta ce idan ba a kare ran Fulani ba, mutanen Kudu ba za su koshi ba

- An tare iyakar Kwara, an hana mutane su wuce da kayan abinci zuwa Kudun

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Association of Cattle Breeders na reshen jihar Kwara, Aliyu Mohammed ya ce za a cigaba da hana kai abinci zuwa kudu.

Alhaji Aliyu Mohammed ya ce za a cigaba da tare kayan abinci da su ka nufi yankin kudu ta jihar Kwara, har sai an tabbatar cewa za a tsare ran Fulanin yankin.

PM News ta ce Mohammed ya bayyana wa manema labarai hakan ne bayan kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah sun yi wani muhimmin taro a Ilorin a ranar Lahadi.

Shugaban kungiyar ya ce sun dauki wannan mataki ne domin ja-kunnen mutanen Kudu a kan cin-kashin da ake yi wa Fulani da su ke neman na abincinsu a waje.

KU KARANTA: Rikicin 'Yan bindiga da abubuwa 3 su ka sa zan yi takara - Okupe

“Akwai bata-gari a ko ina, kamar yadda ake da bara-gurbi da mutanen kwarai a al’umma.” Yake jawabi ya na wanke Fulani daga kudin-goron zargin da ake yi masu.

“Ba Fulani kadai su ke laifi a kasar nan ba, abin haushi ne ace yanzu duk abin da ya faru sai a zargi makiyaya Fulani.” MACBAN ta bukaci a kama Sunday Igboho.

Miyetti Allah ta ce za ta tona asirin duk wani da ya zo jihar Kwara da sunan Fulani, ya na barna.

A jawabin na sa, Aliyu Mohammed ya yaba wa gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, ya ce ko kodan, gwamnatinsa ba ta nuna wa Fulani bambanci a jihar Kwara.

Miyetti Allah na yi wa Yarbawa barazana, ba za a kai masu abinci ba sai an kare Fulani
Dabbobi su na kiwo
Asali: UGC

KU KARANTA: Kayan abinci sun tashi a Kudancin Najeriya

Sannan kungiyar MACBAN ta sha alwashin hada-kai da jami’an tsaro wajen tsefo barayin shanun da su ke fake wa da makiyaya su na aikata ta’adi iri-iri a cikin jejin Kwara.

A baya kun ji irin rawar ganin da Ministan sadarwa da tattalin zamani, Dr. Isa Ali Pantami ya taka wajen kashen wutar rigimar da ta tashi a Oyo inda aka kashe Bayin Allah.

Isa Ali Pantami ya bayyana irin kokarin da ya yi wa Musulmai da ‘Yan Arewa a rikicin Shasha

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi karin-haske a kan rikicin Yarbawa da Hausawa, ya ce sai da ya yi magana da gwamnoni 5.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel