Yajin aiki: Kayayyakin abinci sun yi tashin gwauron zabo a kudancin Najeriya

Yajin aiki: Kayayyakin abinci sun yi tashin gwauron zabo a kudancin Najeriya

- Da alamu janye kai kayan abinci kudancin Najeriya zai tsoma yankin cikin tsananin tsadar abinci

- Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu kayan abinci sai kara farashi suke a kudancin Najeriya

- A bayyane yake karara akasarin kayan abinci a kudu yakan fito ne daga arewacin Najeriya

Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka shiga na kungiyar Hadin kan Dillalan Kayan Abinci da Shanu (AUFCDN), ya janyo hau-hawan farashin kayayyaki a yankin kudancin Najeriya, a cewar rahoton Daily Trust.

Kungiyar ta AUFCDN wacce bangare ne na kungiyar kwadago ta kasa wato (NLC), ta shiga yajin aikin ne a ranar Alhamis biyo bayan karewar wa'adin da ta bai wa Gwamnatin Tarayya na kwana bakwai da ta biya mata bukatunta.

Kungiyar na neman a biya ta diyyar naira biliyan 475 sakamakon Barnar da aka yi wa mambobinta a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma kashe Hausawa 'yan kasuwa da aka yi a rikicin kabilancin da ya auku a kasuwar Shasa ta Jihar Oyo.

KU KARANTA: COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori

Yajin aikin dillalan abinci da shanu ya tsunduma kudancin Najeriya tsadar abinci
Yajin aikin dillalan abinci da shanu ya tsunduma kudancin Najeriya tsadar abinci Hoto: Cokodeal
Asali: UGC

Haka nan ta bukaci a janye dukkan shingen duba ababen hawa daga kan manyan tituna, inda ake cin zarafin mambobinta ta hanyar karbar kudi daga hannunsu ba bisa ka'ida ba.

Yajin aikin ya sa an tsayar da duk wata jigilar kayan abinci daga Arewacin Najeriya zuwa Kudancinta, wadanda suka hada da dabbobin yanka da kuma kayan miya.

Rahoton jaridar ya ce mahautan da ke da nama a jihohin kudu sun yi amfani da wannan damar sun tsauwala farashi, su ma masu kayan miya ba a bar su a baya ba, inda farashinsu ya tashi sosai.

Akasarin kayan abinci da suka hada da nama da kayan gwari, 'yan kasuwa ne kan yi safararsu daga arewacin kasar zuwa kudanci.

KU KARANTA: Matawalle: Zaku sha mamaki idan na tona asirin masu hannu a sace daliban Jangebe

A wani labarin, Jaridar the Tribune ta rawaito farfesa Abiodun Salahu na jami'ar North-West da ke Afirka ta kudu ya bayyana cewa ƙoƙarin hana isar da kayan abinci kudancin ƙasar nan daga Arewa abu ne da bai zai je ko'ina ba.

Ya bayyana hakan ne ga jaridarTribune a ranar Asabar kan rahoton da ke nuna cewa mutanen Arewa, da ke tare motoci cike da kayan abinci wajen hana su wucewa abun mamaki ne da ban dariya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel