Nayi magana da Gwamanoni 5, Minista 1 da aka aukawa mutanenmu a Oyo inji Pantami

Nayi magana da Gwamanoni 5, Minista 1 da aka aukawa mutanenmu a Oyo inji Pantami

- Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce ya kokarta wajen kashe wutan rikicin Shasha

- Ministan ya bayyana irin gudumuwar da ya ba bada ba tare da ya fito ya fada ba

- Da rigimar Shasha ta barke, ya tuntubi wasu Gwamnoni da Mohammad Dingyadi

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi karin-haske a kan rikicin Yarbawa da Hausawa da aka yi a jihar Oyo.

Kamar yadda wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter ya nuna, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce ba duk kokarin da ya yi ne yake fito wa ya bayyana ba.

Ministan yake cewa ya yi magana da wadanda ya dace su duba kadin lamarin da kuma daukar hakki a kan wadanda aka zalunta a rigimar Shasha.

A cewar Ministan, ya tuntubi Gwamnan jihar Oyo, amma bai same shi ba, har ta kai ya yi waya da mataimakin gwamnan akalla sau uku a rana guda.

KU KARANTA: Ana zargin Darektan cibiyar NARICT da kabilanci da son-kai

Ibrahim Pantami ya ke cewa ya na tuntubar manya ne a matsayinsa na ‘Dan Najeriya, musulmi, ‘Dan Arewa.

Dr. Isa Pantami ya ce ya yi wa wadannan mutane bayanin takaicin da 'Yan Arewa su ka shiga da fushi da irin damuwar Musulman yankin su ka shiga.

Pantami ya ce mataimakin gwamnan jihar Oyo ya yi masa karin bayani a kan matakan da hukuma ta dauka, har ya sanar da shi abubuwa da bai sani ba.

Bayan haka, Pantami ya yi magana da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ganin cewa ya na da kishin al’umma, sannan ya aika wa gwamnan Ekiti sako.

KU KARANTA: Femi Fani-Kayode ya yanke shawarar ba zai koma APC ba

Nayi magana da Gwamanoni 5, Minista 1 da aka aukawa mutanenmu a Oyo inji Pantami
Isa Ali Pantami Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Ministan ya tattauna da shugaban gwamnonin Arewa,gwamnan Filato, Simon Lalong da gwamna Babagana Zulum domin ganin yadda za a magance rikicin.

Wani babba da Ministan ya tuntuba shine Ministan harkokin ‘yan sanda, wanda ya taka rawar gani, ya kuma yi alkawarin aika wa mutanen da abin ya shafa tallafi.

A makon da ya gabata ne mataimakin shugaban kasa, FarfesaYemi Osinbajo ya yi kira a sa ido a kan ‘Crypto’, a maimakon a hana amfani da shi gaba daya a Najeriya.

Yemi Osinbajo yake cewa a na sa ra'ayin a ce, an hana cinikin Cryptocrrency gaba-daya bai dace ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel