Hadimin Jonathan da Obasanjo, Okupe ya na harin komawa Aso Villa, ya kudiri takara a 2023

Hadimin Jonathan da Obasanjo, Okupe ya na harin komawa Aso Villa, ya kudiri takara a 2023

- Dr. Doyin Okupe ya bada sanarwar zai nemi kujerar Shugaban kasar Najeriya

- Na-kusa da tsofaffin shugaban kasar ya na ganin abubuwa ba su tafiya daidai

- Doyin Okupe ya bayyana dalilan da su ka sa yake harin zama Shugaban kasar

Dr. Doyin Okupe, wanda ya taba zama Mai ba tsofaffin shugabannin Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo shawara zai yi takara a 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa Doyin Okupe ya bada sanarwar tsaya wa neman takarar kujerar Shugaban kasa a shafukansa na sada zumunta a ranar Juma’a.

‘Dan siyasar ya bayyana wasu dalilansa da yace su ka sa yake sha’awar babbar kujerar Najeriya.

Doyin Okupe yake cewa abubuwa ba su tafiya daidai a kasar nan, sannan ya ce ya na ganin zai iya dawo da Najeriya a kan hanyar da ta dace idan ya samu mulki.

KU KARANTA: Babu ruwan Jonathan da APC a 2023 - Saraki

Ya ce: “Tsakani na da Allah, na yi imani cewa bai kamata abubuwa su rika tafiya a yadda su ke ba.”

“Na yi aiki da manyan shugabannin kasa biyu da aka yi, kuma na kasance kusa da madafan iko, ta yadda zan san abubuwan da ya kamata ayi a wannan yanayi.”

Abubuwan da su ka sa Okupe yake neman mulkin Najeriya su ne:

1. Ana cigaba da fama da ta’adin ‘yan bindiga a fadin kasar nan.

2. An gagara shawo kan matsalar garkuwa da mutane a cikin Najeriya.

3. Miyagun makiyaya su na ta kai hari a Kudu maso yamma.

4. Ta’addancin Boko Haram ya ki zuwa karshe.

Hadimin Jonathan da Obasanjo, Okupe ya na harin komawa Aso Villa, ya kudiri takara a 2023
Doyin Okupe Hoto: Facebook, Doyin Okupe
Asali: Facebook

KU KARANTA: 2023: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a zaben Kano - Kwankwaso

Okupe ya cigaba da bayanin abin da ya sa zai dace da shugaban Najeriya. Ya ce ba yabon-kai ba ne, ya yi imani ya na da ilmi, kaifin tunani, da sanin aikin da zai yi mulki.

A makon da ya gabata, kun ji cewa tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode ya yanke shawarar cewa ba zai rabu da PDP, ya koma jam'iyyar APC mai mulki ba.

Femi Fani-Kayode ya bada dalilan zamansa a PDP, ya ce bai kawo barin PDP ya sauya-sheka zuwa APC ba. Jigon na jam'iyyar hamayya yake cewa barin PDP magana ba ce.

Fani-Kayode ya bayyana cewa an dinke barakar da aka samu da shi a jam'iyyarsu ta PDP.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng