Rikicin makiyaya: Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani kada su dauki AK-47

Rikicin makiyaya: Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani kada su dauki AK-47

- Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani makiyaya kan dan Allah kada su dauki bindigar AK-47

- Ya bukaci su kasance masu zaman lumana kamar yadda aka sansu da kara da mutuntaka

- Ya kuma bayyana bazai nemi gafarar masu sukar Fulanin makiyaya ba ko da kuwa wanene

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya roki Fulani makiyaya da kada su dauki bindiga AK-47 kuma su kasance cikin lumana.

Gwamnan, ya yi wannan rokon a jawabinsa a wajen kaddamar da allurar rigakafin dabbobi na shekara-shekara ta 2020/2021 da aka gudanar a Galambi Cattle Ranch dake Bauchi, ranar Laraba, ya bayyana Fulani a matsayin masu tawali’u, masu sauƙin kai, da kawaici.

Ya ce, “Abin da zan yi, ba zan faɗi shi a nan ba, amma zan yi duk mai yiwuwa don tabbatar da na kare ku da kuma ba ku goyon baya saboda na san kuna da kyau.

KU KARANTA: Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong

Rikicin makiyaya: Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani kada su dauki AK-47
Rikicin makiyaya: Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani kada su dauki AK-47 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

"Ta hanyar lokaci da tarihi, da an ganku an ga abin birgewa, an kuma cutar daku amma kun kasance da mutuntaka.

"Ku kasance masu saukin kai, ba ku nuna fitina da yawa kuma ba shakka, cewa tawali'u ko yaushe abin da muka gani ne tattare daku, kuma wannan shine halin da ko yaushe ya kamata ku nuna.

“Don Allah, kar ku dauki AK-47 din da na yi magana akanta a fasahance. Ku yi ƙoƙari don tabbatar da cewa kun kasance cikin lumana."

Gwamnan ya ce ba zai nemi gafara game da korafe-korafe ba da ake yi wa Fulani makiyaya a matsayin masu laifi ba.

Ya ce gwamnatinsa na sane da ayyukan kungiyar Miyetti Allah da sauran kungiyoyin Fulani wajen inganta zaman lafiya a jihar, inganta zaman lafiyar makiyaya, samar da arziki, da kuma sasanta rikici musamman jihar da kasa baki daya.

KU KARANTA: Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani

A wani labarin, Wadanda ba ‘yan jihar Gombe ba da ke zaune a Jihar musamman wadanda ke cikin karamar Hukumar ta Billiri da rikici ya rutsa da su an ba su tabbacin jajircewar gwamnati ga tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, Nigerian Tribune ta ruwaito.

An shawarci al'ummomin da ke zaune su ci gaba da harkokinsu na halal ba tare da wata fargaba ba ko cin mutuncin wani muddin suka ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel