Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani

Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani

- Bayan ritayar hafsoshin tsaron Najeriya, shugaba Buhari na nada wani matsayi na daban

- A makon da ya gabata ne majalisar dattijai suka tabbatar da matsayin nasu ba tare da dogon zance ba

- Ba a bar sanata Shehu Sani a baya ba wajen to f albarkacin bakinsa dangane da nadin nasu

A yammacin ranar Talata, Shehu Sani, wani tsohon Sanata, ya caccaki Majalisar Dattawa a karkashin jagorancin Ahmad Lawan.

A cikin wani sakon da ya wallafa bayan an tabbatar da tsofaffin shugabannin hafsoshin soji a matsayin jakadodi da shugaba Buhari ya nada, tsohon sanatan cikin raha ya ce za su “su gode wa Allahnsu” cewa ba su yi karo da majalisar dattijai a karkashin Bukola Saraki ba.

KU KARANTA: Alheri ne ga 'yan Najeriya hana kasuwancin Bitcoin, in ji gwamnan CBN

Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani
Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani Hoto: NewsWireNGR
Asali: UGC

Yayin da magoya bayan tsohon hafson tsaro, Gabriel Olonisakin; tsohon shugaban hafsin soji, Tukur Buratai; tsohon Shugaban Sojojin Sama, Abubakar Sadique da kuma tsohon Shugaban Sojojin Ruwa, Ibok Ibas, sun yi murna, masu sukar majalisar dattijai su ma sunyi.

KU KARANTA: Rikicin addini a Gombe: Ba zan lamunci aikata ta'addanci a jiha ta ba, gwamna Inuwa

A wani labarin, Majalisar dattijai ta fara tantance sabon Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, Vanguard ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar da Bawa wanda tuni ya kasance a dakin taron.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel