Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong

Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong

- Kungiyar manoma a jihar Filato ta musanta zargin da gwamnan jihar yayi kan mallakar bindiga kirar AK-47

- Kungiyar ta bayyana cewa bata taba samun karar wani manomi da ake zargi da daukar makami ba

- Hakazalika kungiyar ta bayyana cewa mambobinta basa taba husuma a fadin jihar ta filato

Manoma a jihar Filato sun caccaki gwamnan jihar Simon Lalong kan zargin da yake musu na mallakar bindigogi kirar AK-47 kamar yadda Fulani makiyaya suke, jaridar Punch ta tattaro.

Lalong ya bayyana haka ne lokacin da yake magana a shirin gidan talabijin na Channels TV, Sunrise Daily a ranar Talata, ya ce ba daidai bane a tasa Fulani makiyaya a gaba kadai ba da zargin mallakar bindigogin AK-47 kasancewar manoma ma suna dashi.

KU KARANTA: Kimanin 'yan Najeriya miliyan 87 ke fama da matsanancin talauci, AfDB

Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong
Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong Hoto: Freedom Radio Nigeria
Asali: UGC

Gwamnan ya ce, “Ba ina bayar da hujjar kowa ya dauki AK-47 bane, amma kar ku manta cewa a yayin gudanar da bincike da kwakkwafi, ba Fulani makiyaya ne kadai ke yawo da AK-47 ba, har ma manoma suma suna da AK-47. ”

Haka nan, Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Filato (AFAN), John Wuyep, ya bayyana kalaman a matsayin zunzurutun karya. Shugaban ya ce:

“Kamar yadda mutane suke da 'yancin kare kansu, babu wani manomi, a iyakar sanina, da aka taba kama shi saboda yana dauke da makamai da alburusai ba ma batun AK- 47 ba.

“Manoma a jihar masu bin doka ne; suna gudanar da harkokin su cikin lumana kuma kungiyar manoma ba ta taba samun karar wani manomi da aka kama da AK 47 ko wani makami ba. ”

KU KARANTA: CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin

A wani labarin, Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta samar da wuraren kiwo ga makiyaya wadanda ke son kafa kasuwanci a jihar, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya ce jihar Borno na da filin noma mai fadin kusan kilomita murabba'in dubu 73 wanda zai iya daukar yawan makiyaya.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin a yayin kaddamar da fara aikin gaggawa na Hukumar Kula da Yankin Arewa-maso-Gabas a Maiduguri.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel