Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Oyo ya bada umarnin sake bude kasuwar Sasha a yau

Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Oyo ya bada umarnin sake bude kasuwar Sasha a yau

Yanzu-yanzun nan Gwamnan Makinde na jihar Oyo ya sake buɗe kasuwar Sasha bayan rufe ta na tsawon kwanaki biyo bayan rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Yarbawa a cikin kasuwar.

Mun ruwaito muku irin asarar da aka tafka a yayin rikicin tare da rayukan da rikicin ya hallaka.

Don samun zaman lafiya ya dawo cikin al’ummar Shasha, biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Yarbawa da Hausawa a kasuwar, Gwamna Seyi Makinde, a safiyar ranar Talata, ya ba da umarnin sake bude kasuwar ba tare da bata lokaci ba.

An sami umarnin sake bude kasuwar ne a yayin ganawa da shugabannin Al’ummar Shasa, wanda aka gudanar a dakin taro na Western Hall a Sakatariya dake Ibadan.

Karin bayani nan kusa...

Source: Legit.ng

Online view pixel