Zamu daina kai shanu kudu idan gwamnati bata dauki mataki kan kashe mu ba, Dillalan shanu

Zamu daina kai shanu kudu idan gwamnati bata dauki mataki kan kashe mu ba, Dillalan shanu

- Dillalan shanu a Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da kashe mambobinsu a kudu

- Dillalan sun yi ikirarin shiga yajin aiki matukar gwamnati bata dauki mataki kan barnar ba

- Hakazalika, sun bada wa'adin kwanaki 7 domin shawo kan lamarin ko kuma su runtuma yaji

Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da kalubalen tattalin arziki, yanzu kuma dillalan shanu na barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar.

Hadaddiyar kungiyar dillalan abinci da shanu ta Najeriya (AFUCDN) ta nuna rashin jin dadin ta da cewa ana kashe mambobinta a sassa daban-daban na kasar.

Shugabanin kungiyar kwadagon a ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairu, sun ce suna ba gwamnati zuwa ranar 24 ga Fabrairu, don magance matsalolinsu ko kuma za su fara yajin aikin a masana'antu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Har yanzu ba’a sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara ba

Dillalan shanu na barazana ga gwamnati kan shiga yajin aiki
Dillalan shanu na barazana ga gwamnati kan shiga yajin aiki Hoto: World Bank Group
Asali: UGC

Wata sanarwa da AFUCDN ta fitar ta yi zargin cewa an kai hare-hare ba kakkautawa kan mambobinsu da kadarorinsu a duk fadin kasar tun bayan zanga-zangar #ENDSARS a watan Oktoba na shekarar 2020.

Ahmed Alarama, babban sakataren kungiyar, ya yi ikirarin cewa an kashe wasu mambobinsu tare da lalata dukiyoyinsu a rikicin kwanan nan da ya faru a yankin Shasha da ke garin Ibadan, jihar Oyo.

Ya bayyana cewa kungiyar kwadagon ta rubutawa gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, sarakuna masu daraja ta daya, da sauran su game da bala'in nasu amma ba su samu amsa ba.

Kungiyar ta ce suna neman gwamnatin Najeriya da ta kulla yarjejeniya tsakanin jihohi 36 da AFUCDN.

Alarama ya ci gaba da lura cewa idan ba a yi komai ba a karshen wa'adin kwanaki bakwai din, kungiyar za ta yi kira ga mambobinta da su dakatar da zirga-zirgar shanunsu da kayayyakinsu a duk fadin kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe

A wani labarin, Bayan fada tsakanin Yarbawa da Hausawa a kasuwar Shasha da ke Ibadan, asarar ta ratsa kabilun biyu; hatta shugabanni a cikin al'umma sun yi asarar da ta wuce lissafi.

Amma mako guda bayan mulkin tashin hankalin, kabilun biyu sun taru a karkashin rufi daya don yin sallar jam'i ta Juma'a aranar Juma'a.

Rashidi Muraina, babban limamin da ya jagoranci sallar a babban masallacin kasuwar Shasha, ya shaida wa TheCable cewa da an kauce wa rikicin idan da wadanda abin ya shafa sun yi hakuri.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.