Elon Musk ya rasa N5trn dalilin Bitcon ya sauka daga matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya
- Wanda ya fi kowa kudi a duniya ya sauka daga matsayinsa a jiya Litinin 22 ga Fabrairu
- Elon Musk ya tafka asarar makudan kudade sakamakon haurawar kudaden Intanet
- Dan kasuwan ya rasa kimanin kudin Najeriya tiriliyan 5 sakamakon tafka asarar
Babban jami'in kamfanin Tesla, Elon Musk, ya sauka daga matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a duniya; shugaban kamfanin Amazon ya karbe matsayin, Legit.ng ta gano.
A cewar Bloomberg, hannun jarin Tesla ya fadi kasa da kashi 8.6% a ranar Litinin, 22 ga Fabrairu, tare da rasa dala biliyan 15.2 (N5,795,000,000,000) daga dukiyar Musk.
Daya daga cikin dalilan raguwar shi ne maganganun Musk a ƙarshen mako cewa farashin Bitcoin da Ether "da alama sun cilla sama".
KU KARANTA: Farashin man fetur zai iya cillawa zuwa N200, sakamakon tashin farashin danyen mai zuwa $64
Sakon nasa ya zo makonni biyu bayan Tesla ya sanar da cewa ya sayi dala biliyan 1.5 (N571,875,000,000) na Bitcoin.
Elon Musk yanzu ya mallaki kudin da ya kai dala biliyan 183.4 yayin da darajar kudin Jeff Bezos ta kai dala biliyan 186.3.
KU KARANTA: Mata a Saudiyya sun sami 'yancin shiga aikin soja a kasar
NERC, wacce ta amince da karin kudin da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ta fitar, ta ce karin ya kasance tsakanin N2 zuwa N4, amma wani bangare na masu amfani da wutar da suka sake cajin mitocin su kwanan nan, sun nace cewa karin ya haura N4.
Aminiya ta tattauna da ’yan Najeriya don gano yadda hawan ya shafi amfani da wutar lantarki da suke yi.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng