Gombe tana da mafi yawan wuraren kiwo a Afirka, in ji Gwamna Yahaya
- Gwamnan jihar Gombe ya bayyana cewa jihar ta Gombe ta kasance ta mallaki mafi girman filin kiwo a Afrika
- Gwamnan ya bayyana hakane ga ministan jiha na ma'aikatar noma ta kasa a wani yayin shiri a Gombe
- Gwamnan ya kuma roki gwamnatin tarayya kan kara bada hadin wajen ciyar da yankin arewa maso gabas gaba
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce jihar Gombe itace jihar da ke da mafi yawan wuraren kiwo a Afirka, jaridar Punch ta ruwaito.
Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, yayin da yake karbar bakuncin Ministan jiha na Aikin Gona, Mustapha Shehuri, wanda ya je jihar don kaddamar shirin bayar da kayan gona ga kananan manoma na amfanin gona 14 don rage illar cutar COVID-19.
Ya ce, “An albarkace mu da dam din Dadinkowa, an albarkace mu da dam din Balanga, da kuma dam din Cham da sauran gabar ruwan Kogin Gongola, wannan ya sa jihar ta zama mai amfani sosai ga harkar noma.
"A saman wannan, muna da wurin kiwo mafi girma a duk fadin Afirka, Wawa Zange wurin kiwo wanda ya kai hekta 144,000."
KU KARANTA: Baya ga Najeriya, akwai kasashe bakwai da suka haramta cinikin Bitcoin
Yayin da yake kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara bada hadin kai, Yahaya ya jaddada cewa jihar na fama da babban nauyi sakamakon yankin da take.
“Hakan ya kawo matukar damuwa a kan albarkatunmu; aikin gona, kiwon lafiya, kayayyakin more rayuwa, samar da ruwa da sauransu.
"Hakan ya sanya mu cikin rauni sosai kuma muna bukatar goyon bayan ma'aikatar noma ta tarayya da dukkanin ma'aikatun tarayya, sassa da hukumomi domin mu ci gaba da sauke wannan nauyi na 'yan gudun hijira da kuma kula da hanyoyin rayuwar mutanenmu.
"Kashi saba'in da biyar ko 80% na mutanenmu manoma ne, manoma wadanda sun kai kimanin mutane miliyan 3.5, ” in ji gwamnan.
A nasa bangaren, Shehuri ya ce ya zo jihar ne don kaddamar da shirin bayar da kayan gona don tallafawa manoma musamman ma, mata daidai da Tsarin Aikin Jinsi na Kasa da Manufofi da nufin samar da karin dama ga mata.
KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata
A wani labarin, Akalla mambobi dari uku na majalisar jihar Gombe na kungiyar 'yan fansho ta Najeriya a ranar Laraba suka toshe babbar kofar shiga gidan gwamnatin jihar ta Gombe lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa a yankin, jaridar Punch ta ruwaito.
A cewar Mohammed Abubakar, shugaban karamar hukumar a tattaunawar da yayi da manema labarai, yan fanshon suna zanga-zangar rashin biyansu kudaden fansho da ya kwashe watanni.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng