Ta yiwu a sako dalibai da ma'aikatan GSSS Kagara yau Lahadi, in ji Gumi

Ta yiwu a sako dalibai da ma'aikatan GSSS Kagara yau Lahadi, in ji Gumi

- Fitataccen malamin addinin Islama Sheikh Gumi ya bayyana yiyuwar sakin yaran GSSS Kagara a yau Lahadi

- Malamin ya shaida cewa, tattaunawarsa da 'yan bindigan ya nuna yiyuwar sakin daliban da malamansu

- Ya kuma bayyana cewa babu batun biyan kudin fansa a cikin sharadin sakin yaran da nasu malaman

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Gumi, ya fada a ranar Asabar cewa watakila za a sako daliban makarantar Kagara da aka sace a yau Lahadi, ganin yadda tattaunawa ke gudana tsakanin gwamnati da 'yan fashin.

Malamin, wanda ke iya shiga dazuka domin tattaunawa, nasiha da wa'azi ga manyan 'yan bindigan da yaransu, ya shaidawa manema labarai yiyuwar sakin daliban da ma'aikatan makarantar a jiya Asabar.

An ruwaito Malamin yana bayanin cewa, a tattaunawarsa da 'yan bindigan, basu bayyana bukatarsu ga kudin fansa ba.

KU KARANTA: Ba kudin fansa 'yan bindiga suke nema ba kafin su sako daliban Kagara, in ji Sheikh Gumi

Ta yiwu a sako dalibai da ma'aikatan GSSS Kagara yau Lahadi, in ji Gumi
Ta yiwu a sako dalibai da ma'aikatan GSSS Kagara yau Lahadi, in ji Gumi Hoto: Greenbarge Reporters
Asali: UGC

A cewarsa, 'yan bindigan na bukatar a saki wasu daga cikin mutanensu da aka kame ne, kuma a shirye suke domin tuba da jefar da makamansu matukar gwamnati zata yafe musu.

Malamin a baya ya shiga dazukan yankin Zamfara da Katsina domin tattaunawa da shugabannin 'yan bindigan, wanda kuma ya haifar da da mai ido kasancewar samun wasu daga cikin 'yan bindigan sun tuba sun aje makamansu.

Ya shaida wa daya daga cikin wakilan Punch cewa tattaunawar da aka yi game da sakin yaran makarantar da ma'aikatan ta yi tafiyar hawainiya ne saboda kokarin shirya kayan aikin jigilarsu, amma ana sa ran sakinsu a yau Lahadi.

Da aka tambaye shi ko tattaunawar ta shafi kudi, sai Gumi ya ce, “A’a, a’a; ba haka bane. Idan ya shafi kudi, yana nufin aikata laifi iri daya.

"Suna cewa wadannan su ne sharuddanmu kuma za mu dakatar da wannan abu. Don haka, tattaunawa tana gudana kuma ana duba bukatunsu, wadanda suke da sauki sosai.”

KU KARANTA: Yanzun nan: 'Yan sanda sun fara sintiri da jiragen sama don gano daliban da aka sace a Kagara

A wani labarin, Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba 'yan fashi da ke son yin sulhu idan har za a magance matsalar tsaro a yanzu.

Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel