Yanzun nan: 'Yan sanda sun fara sintiri da jiragen sama don gano daliban da aka sace a Kagara

Yanzun nan: 'Yan sanda sun fara sintiri da jiragen sama don gano daliban da aka sace a Kagara

- Rundunar 'yan sandan Najeri=ya sun shiga sintiri da jiragen sama don ceto daliban Kagara

- Rundunar ta bayyana cewa ta dukufa sai ta gano inda dalibai da ma'aikatan makarantar suke

- Suna kuma bukatar hadin kan jama'a kan bada bayanai masu amfani don saukake ceton

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aikin ceto ta sama don ceto daliban da aka sace, malamai, da sauran ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.

Kakakin ‘yan sanda, Frank Mba, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken: Satar Kagara: Mun dukufa wajen ganin mun kubutar da duk wadanda aka sace, in ji IGP’, a ranar Alhamis.

Mba ya kuma ce tuni aka fara sa ido a iska don ganin an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

KU KARANTA: Tsoron sace dalibai: Gwamnatin jihar Osun ta garkame makaranta

Yanzun nan: 'Yan sanda sun fara sintiri ta sama don gano wadanda aka sace a Kagara
Yanzun nan: 'Yan sanda sun fara sintiri ta sama don gano wadanda aka sace a Kagara Hoto: The Whistler NG
Asali: UGC

Sanarwar da hukumar 'yan sanda ta kasa ta wallafa a shafin Twitter ta ce:

"Sufeto-janar na‘ yan sanda, MA Adamu, ya tabbatar wa da kasa cewa rundunar ta dukufa don ceto duk wadanda aka sace a harin baya-bayan nan da aka kai a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara da sauran abubuwan da suka shafi hakan.
“IGP din ya lura da cewa hadin gwuiwar bincike da ceto wadanda suka hada da 'yan sanda, Soja, da sauran jami’an tsaro na ci gaba da tabbatar da cewa an ceto dukkan mutanen da aka sace ba tare da rauni ba kuma sun hadu da danginsu.
"Sufeto-Janar na 'yan sanda, yayin da yake kira da a kwantar da hankula, ya umarci mambobin al'umman da su bai wa rundunar tsaro bayanai masu amfani, dasuka dace, kuma a kan lokaci da za su iya taimakawa a cikin aikin bincike da ceto."

KU KARANTA: Rashin nuna kwarewar jami'an tsaro ke jawo sace dalibai, in ji Solomon Dalong

A wani labarin, Biyo bayan hari da kuma sace dalibai da ma'aikatan makarantar Kagara dake jihar Neja, masana harkokin siyasa, tsaro da lamuran yau da kullum sai fadan albarkacin bakinsu suke.

Daya daga cikinsu, wani tsohon sanata a jihar Kaduna, Shehu Sani da ya shahara wajen sharhi kan lamuran siyasar yau da kullum, ya tofa albarkacin bakinsa dangane sace daliban, yana mai sharhi kan yadda yanayin ginin makarantar yake.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel