Yanzu-yanzu: Gwamnan Niger ya rufe makarantun kwana a ƙananan hukumomi huɗu

Yanzu-yanzu: Gwamnan Niger ya rufe makarantun kwana a ƙananan hukumomi huɗu

- Gwamnatin jihar Niger ta bada umurnin a rufe dukkan makarantun kwana da ke yankunan da ke cikin hatsari a jihar

- Gwamnan jihar Abubakar Sani-Bello ya bada wannan umurnin ne biyo bayan harin da yan bindiga suka kai kwallejin kimiyya ta Kagara

- A yayin harin, yan bindigan sun halaka dalibi daya sannan sun yi awon gaba da wasu dalibai 27, ma'aikata uku da iyalansu 12

Gwamna Sani Bello na jihar Niger ya bada umurnin rufe makarantun kwana da ke wasu kananan hukumomi hudu na jihar nan take, Daily trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan sace wasu dalibai da ma'aikatan makarantar kwallejin Kimiyya ta gwamnati da ke Kagara.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari GSC Kagara a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu

Yanzu-yanzu: Gwamnan Niger ya rufe makarantun kwana a ƙananan hukumomi huɗu
Yanzu-yanzu: Gwamnan Niger ya rufe makarantun kwana a ƙananan hukumomi huɗu
Asali: Original

Yan bindiga sun afka makarantar a daren ranar Talata sun sace dalibai da kuma wasu ma'aikatan makarantar.

KU KARANTA: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

Wani dalibi ya rasa ransa sakamakon harbe harben da yan bindigan suka yi yayin harin.

Da ya ke yi wa yan jarida jawabi a Minna, babban birnin jihar, Bello ya bada umurnin a rufe dukkan makarantun kwana da ke kananan hukumomin Rafi, Munya, Mariga da Shiroro nan take.

Gwamnan ya yi kira ga al'umma su taimakawa jami'an tsaro da bayanai da za su taimaka wurin ceto wadanda abin ya shafa.

Bello ya ce dalibai 27, ma'aikata uku da iyalansu 12 ne yan bindigan suka sace.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel