Gwamnonin Arewa ga mutanen Arewa: Kada ku kai wa ‘yan kudu hari a arewa
- Shugabannin Najeriya sun farka ga aikin rage tashin hankali a wasu sassan kasar
- Gwamnonin arewacin Najeriya na kan gaba wajen tabbatar da cewa rikicin kabilanci da ya barke a yan kwanakin nan a jihar Oyo bai haifar da daukar fansa ba a arewa
- An bukaci yan asalin arewacin Najeriya da suyi taka tsan-tsan da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiyar da ake gani a halin yanzu
Kungiyar gwamnonin Arewa (NSGF), a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu sun bukaci mutanen arewacin Najeriya da kar su dauki fansa kan ‘yan kudu da ke zaune a kowane yanki na arewa saboda rikicin kabilanci da ake fuskanta a wasu sassan jihar Oyo.
Kungiyar ta lura cewa irin wannan matakin ba zai magance matsalar da kasar ke fuskanta ba a yanzu, amma zai kara fadada ta.
Sai dai kuma, kungiyar ta NSGF, ta ba mutanen Arewa tabbacin cewa tana yin duk abunda ya dace don magance matsalar da ta shafi wasu ‘yan arewa a jihar Oyo.
Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato wanda shi ne shugaban kungiyar ya yi wannan rokon yayin ganawa tsakanin kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da NSGF a masaukin gwamnan Filato da ke Abuja.
KU KARANTA KUMA: Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu
Jaridar Daily Trust ta ambato shi yana cewa:
“Wannan taron ya zama dole kuma ya zama wani bangare na tattaunawarmu tun lokacin da batun barazanar wa’adin barin gari ya fara daga kungiyoyi daban-daban a kasar.
“Mun tattauna da shugabanni daga arewa don nemo mafita da kwantar da tashin hankalin da ke faruwa a yanzu sakamakon rikicin da ya barke a jihar Oyo.
“Babu wata fa’ida a daukar fansa kan ‘yan kudu da ke zaune a arewa. Mun tura wakilai zuwa Oyo don sanin halin da ake ciki da gaskiyar abin da ya faru.
“Da yardar Allah za mu kai ga tushen matsalar. Kasar ta dukkanin mu ce. Ba ma so mutane su ce wasu su bar yankin. Wannan sam sam ba za a yarda da shi ba.”
A wani labarin, Babban Atoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ba da shawarar a kirkiro wata hukuma ta Gwamnatin Tarayya da za ta kula da ayyukan makiyaya.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Tsohon Shugaban kasa ya yi martani a kan tashin hankalin da ke kasar
Malami ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako na musamman a taron zaman lafiya, hadin kai, da tsaro a babban dakin taro na ECOWAS, Abuja a ranar Talata.
Ministan ya yarda cewa rikicin tsakanin makiyaya da manoma ya zama wani al’amarin gaske kuma akwai bukatar daukar matakai don magance shi, Jaridar Punch ta ruwaito.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng