Malami ya shawarci FG da ta kirkiro hukumar kula da ayyukan makiyaya
- An bukaci gwamnatin Buhari da ta tsara ayyukan makiyaya ta hanyar kirkirar wata hukuma a kan haka
- Ministan shari’ar kasar, Abubakar Malami ne ya yi wannan kiran
- A cewarsa, rikici tsakanin makiyaya da manoma ya zama babban al’amari
Babban Atoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ba da shawarar a kirkiro wata hukuma ta Gwamnatin Tarayya da za ta kula da ayyukan makiyaya.
Malami ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako na musamman a taron zaman lafiya, hadin kai, da tsaro a babban dakin taro na ECOWAS, Abuja a ranar Talata.
Ministan ya yarda cewa rikicin tsakanin makiyaya da manoma ya zama wani al’amarin gaske kuma akwai bukatar daukar matakai don magance shi, Jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu
Ya kuma ce akwai bukatar sake farfado da Hukumar Ilimin Noma.
Ya bayyana cewa, “Najeriya galibi ta ta’allaka ne ga harkar. Har ta kai ana yawan samun makiyaya a koyaushe a cikin yankuna daban-daban na Najeriya. Wataƙila lokaci yayi da za a yi la’akari da kafa kwamitin kula da kiwon dabbobi wanda doka za ta dunga kula da ita.
“Wannan na iya samar da maslaha ga rikice-rikicen manoma da makiyaya. Koma kwamitin na iya shiga ko saukaka zurfin nazari da nufin samar da dawwamammen mafita don amfanin mutane da kasar. ”
Ya kuma yi kira da "sake fasalta ayyukan Hukumar Kula da Ilimin Noma tare da nufin taimakawa kokarin da gwamnati ke yi na magance rikicin manoma da makiyaya."
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Tsohon Shugaban kasa ya yi martani a kan tashin hankalin da ke kasar
A wani labarin, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fito fili ya yi Allah wadai da ayyukan ta’addanci da miyagun makiyaya ke yi.
A cewar jaridar The Nation, Akeredolu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, a yayin wata hira a gidan talabijin na Channels TV.
Gwamnan ya roki hukumomin tsaro da su yi iya bakin kokarinsu wajen hana makiyaya aikata ayyukan ta’addanci.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng