Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

- Kungiyar matasan Arewa sun shawarci 'yan Arewa da su dakata da zuwa Kudu maso yamma

- Kungiyar ta yi Allah wadai da hare-haren da ke ta faruwa a yankin na Kudu maso yamma

- Hakazalika ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan lamurran

Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya (NYCN) ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake zargin ‘yan Arewa da kai wa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Najeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa 'yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.

A kasuwar ne "inda aka kashe mutane rayuka ko jikkata su, yayin da wasu 'yan daba na Yarbawa suka kone wuraren kasuwanci da motoci.

KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai saboda saba dokar Korona

Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa
Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

"Muna yin Allah wadai da wannan harin da kakkausan lafazi sannan kuma muna kira ga jami'an tsaro da su kamo wadanda suka aikata hakan ta yadda za a dakile ayyukan 'yan daba."

Matasan Arewa sun lura da boyayyar manufar da ake da ita na korar ‘yan Arewa mazauna yankin da aka fara tare da yin kira ga dukkan makiyaya da gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, da su bar Mazaunan Gandun Dajin jiharsa.

Matasan sun lura: “Umurnin korar mutanen ya saba wa tanade tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (1999 da aka yi wa kwaskwarima) .

Kundin tsarin mulkin a cewarsu "ya ba da 'yancin yin zirga-zirga ga dukkan ‘yan kasa da kuma 'yancin mallakar kadarori masu motsi da marasa motsi a kowane bangare na kasar.

"Mun yi imanin cewa rashin iyawar gwamnati a dukkan matakai na shawo kan fuka-fukan Sunday Igboho da abokan tafiyarsa ya haifar da ire-irensa.

"Hakan ya jawo, sabbin hare-hare kan 'yan kasuwar da ke zaune da kuma wasu da yawa da ba su iya magana da Yarbanci a Kasuwar Sasha,” in ji sanarwar.

Matasan sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana kungiyar ta Sunday Igboho a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda tunda ba shi da bambanci da Boko Haram.

KU KARANTA: Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN

A wani labarin, Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wani rikici da ya faru sanadiyyar kisan wani mai gyaran takalma da wani mai dakon kaya ya yi a kasuwar Sasha, Ibadan, Jihar Oyo, ya rikide zuwa rikicin kabilanci.

An tabbatar da cewa wanda aka kashen ya mutu ne a asibiti a safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya haifar da rikici tsakanin al’ummar Hausawa da Yarbawa, inda Yarbawan ke kokarin daukar fansar mutuwar dan nasu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel