IGP ya tura rundunonin 'yan sandan kwantar da tarzoma Oyo

IGP ya tura rundunonin 'yan sandan kwantar da tarzoma Oyo

- IGP na 'yan sandan Najeriya ya tura rundunonin 'yan sanda domin kwantar da tarzoma zuwa jihar Oyo

- Rundunonin sun hada da 'yan sandan leken asiri da sauran kwararru don gano asalin rikicin

- IGP ya bayyana wannan yunkuri da neman kawo zaman lafiya da kare rayukan jama'a a yankin

Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura rundunoni hudu na 'yan sandan kwantar da tarzoma don magance rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan jihar Oyo, The Punch ta ruwaito.

Shiga tsakani da rundunar kwantar da tarzomar sun hada da jami'an Ofishin Leken Asirin na kasa da kuma helikopta mai sa-ido guda daya daga sashen jigilar 'yan sanda.

Jihar ta Oyo ta kasance cikin rikici a kwanan nan, ciki har da kashe-kashen da ake zargin makiyaya da yi wa manoma, sace mutane da rikici tsakanin wasu ‘yan kasuwar Hausa da Yarbawa a kasuwar Shasha.

KU KARANTA: Hukumar tsaro ta sojin Najeriya za ta fara daukar aiki a yau Litinin

IGP ya tura rundunonin 'yan sandan kwantar da tarzoma guda hudu zuwa Oyo
IGP ya tura rundunonin 'yan sandan kwantar da tarzoma guda hudu zuwa Oyo Hoto: Vanguard News
Source: UGC

Amma mai magana da yawun rundunar, CP Frank Mba, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai taken, 'Oyo crisis: IGP deploys intervention and stabilization forces, ya ce jami'an za su karfafa tsaro da kuma karfafa gwiwar jama'a kan yankunan da rikicin ya shafa.

Sanarwar ta ce, “Turawar, wadanda suka kunshi yawancin bayanan leken asiri da kayan aiki na rundunar, sun hada da rundunoni hudu na 'yan sanda masu motsi, da kwararrun jami’ai daga Ofishin Leken Asirin na ‘yan sanda.

Hakazalika sanarwar ta kare da cewa, an tura "helikoptar 'yan sanda na aiki/sa ido daga sashen ‘yan sanda na Sashin Sama."

"Mataimakin rundunar Sufeto Janar na 'yan sanda, David Folawiyo ne ya ke jagorantar rundunar da za ta shiga tsakani, wanda ake sa ran zai tattara duk masu ruwa da tsaki don cimma nasarar rundunar."

Sanarwar ta ce IG ya bayar da tabbacin cewa rundunar ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa a jihar.

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m

A wani labarin, Don bayyana goyon baya ga makiyaya wadanda ke dauke da bindigogin AK-47, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya fuskanci shan suka daga mutane a duk bangarorin siyasa wadanda suka bayyana kalaman nasa da "rashin kulawa da tunzura jama'a."

Mohammed ya ba da hujjar daukar muggan bindigogi da makiyaya ke yi da nufin kare kai daga barayin shanu da sauran barazana, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel