Okonjo-Iweala za ta zama mace kuma 'yar Afrika ta farko a matsayin DG na WTO a yau

Okonjo-Iweala za ta zama mace kuma 'yar Afrika ta farko a matsayin DG na WTO a yau

- Kungiyar Ciniki ta Duniya a yau zata nada Okonjo-Iweala a matsayin Darakta Janar na WTO

- Bayan da ta ci zaben da kungiyar ta gabatar a bara, a yau ne za a tabbatar da ita a matsayin

- Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko kuma 'yar Afrika ta farko da za ta rike wannan matsayi

Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO) ta shirya wani taro na musamman na Babban Taronta a ranar Litinin (a yau), inda ake sa ran za a bayyana tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a hukumance a matsayin Darakta Janar.

A cewar sanarwar da jaridar THISDAY ta gani a makon da ya gabata, ajandar taron na yau ita ce, "yin la’akari da nadin sabon Darakta-Janar na WTO.”

Makon da ya gabata gwamnatin Amurka ta ba da izinin ta na musamman ga fitowar Okonjo-Iweala a matsayin Darakta Janar ta gaba.

KU KARANTA: Buhari yana kokarin gyara matsalolin Najeriya, in ji Amb Yabo

WTO za ta tabbatar da Okonjo-Iweala a matsayin DG a yau Litinin
WTO za ta tabbatar da Okonjo-Iweala a matsayin DG a yau Litinin Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Ta kuma yadda ta cire cikas na karshe ga yunkurin ta na zama mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da za ta gudanar da kungiyar kasuwanci ta duniya a ofishinta dake Geneva.

Okonjo-Iweala a watan Oktoban da ya gabata ta samu nasarar kuri'a na mambobi 163 daga cikin 164 na kungiyar cinikayyar, amma ba a iya ayyana ta a matsayin shugabar WTO ba saboda dokokin zaben kungiyar sun nuna cewa dole ne DG nata ya fito ta hanyar yarjejeniya.

Yoo Myung-hee na Koriya ta Kudu, wanda Amurka ke marawa baya, ya kasance abokin hamayyar Okonjo-Iweala bayan wasu ‘yan takarar sun janye daga takarar a bara.

Sai dai Myung-hee a kwanan nan ta sanar da ficewar ta daga takarar, bayan tattaunawa da Amurka da sauran manyan kasashen.

KU KARANTA: Obasanjo ga shugabannin Afirka: Kada ku bari COVID-19 ta hana aiwatar da AfCFT

A makon da ya gabata, mun ruwaito muku cewa Babban Kwamitin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, WTO, ya ce zai duba yiwuwar nada Darakta-Janar na gaba mako mai zuwa ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ku tuna cewa tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, ita ce 'yar takara tilo da ta bayyana a wannan matsayi, biyo bayan sauka daga wani dan takarar wanda ya kasance Minista a Koriya a makon da ya gabata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel