Shugaba Buhari: Okonjo-Iweala ta daga sunan Najeriya a duniya

Shugaba Buhari: Okonjo-Iweala ta daga sunan Najeriya a duniya

- Shugaban kasar Najeriya ya bayyana farin cikinsa a sabon nadin da aka yiwa Okonjo-Iweala

- Shugaban ya nuna farin cikinsa a madadin 'yan Najeriya baki daya wajen yi mata murnar

- Ya kuma bayyana kwarin gwiwa da yake dashi na kawo ci gaba da Okonjo-Iweala zata kawo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohuwar Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, murnar zaben ta a matsayin Darakta Janar (DG) na Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar a madadinsa, Shugaba Buhari ya ce zabenta ya kawo farin ciki da karin daraja ga kasar.

Shugaban ya ce tarihin rayuwarta, kwazo da son ci gaba zai ci gaba da samar da sakamako mai kyau da amfanar dan adam.

Sanarwar ta bayyana murnar shugaban kasan kansa da yayi a madadin daukacin mutanen Najeriya.

KU KARANTA: An ceto fasinjoji 45 a yayin da wuta ta kama wata motar bas a Legas

Shugaba Buhari: Okonjo-Iweala ta daga sunan Najeriya a duniya
Shugaba Buhari: Okonjo-Iweala ta daga sunan Najeriya a duniya Hoto: PM News Nigeria
Source: UGC

"Shugaba Muhammadu Buhari ya yi matukar maraba da tsohuwar Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Dokta Ngozi Okonjo-Iweala a kan zabenta a matsayin Darakta Janar ta Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, wanda ke kawo farin ciki da karin daraja ga kasar.

“Kamar yadda masaniya daga Harvard kuma mashahuriyar masaniyar tattalin arziki ta sake daukar wani aiki mai wahala na yiwa duniya da dan adam hidima,

"Shugaban kasa ya yi imanin cewa tarihinta na mutunci, kwazo da son ci gaba zai ci gaba da samar da sakamako mai kyau da amfanar dan adam.

“Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa Dokta Okonjo-Iweala, wacce a tsawon shekaru ta kafa babban tarihi game da sake fasalin tattalin arziki a Najeriya a matsayin Ministar Kudi, sannan daga baya ta zama Ministan Harkokin Waje,

"Za ta yi fice a sabon mukamin na ta da kuma tabbatar da dokar duniya ta sake sanyawa da karfafawa ƙungiyoyi da yawa don mafi alherin duka.

"Shugaban kasan ya hada kai da dangi, abokai da abokan aikin sa wajen yi wa Dakta Okonjo-Iweala fatan alheri a cikin sabon aikin ta," in ji shi

KU KARANTA: IGP ya tura rundunonin 'yan sandan kwantar da tarzoma Oyo

A wani labarin, Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO) ta shirya wani taro na musamman na Babban Taronta a ranar Litinin (a yau), inda ake sa ran za a bayyana tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a hukumance a matsayin Darakta Janar.

A cewar sanarwar da jaridar THISDAY ta gani a makon da ya gabata, ajandar taron na yau ita ce, "yin la’akari da nadin sabon Darakta-Janar na WTO.”

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel