An ceto fasinjoji 45 a yayin da wuta ta kama wata motar bas a Legas
- An ceto wasu fasinjoji da suka tsallake rijiya ta baya a cikin wata motar bas da ta kone
- Fasinjojin 45 sun makale an ceto su ba tare da rauni ko rasa rai ba yayin gobarar da ta kama
- Rahoto ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a yankin Idiroko-Anthony dake jihar Legas
An ceto fasinjoji arba'in da biyar a ranar Litinin bayan da gobara ta cinye motar Bus din Rapid Transport da ke daukar mutane.
Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin gobarar ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a kusa da yankin Idiroko-Anthony na jihar Legas.
An gano cewa motar BRT din na kan hanyar zuwa tashar TBS dake Lagos Island daga tashar Ikorodu.
KU KARANTA: Makiyaya da AK-47: Baka cancanci zama gwamna ba, Akeredolu ga gwamnan Bauchi
Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa motar farko da ke dauke da fasinjojin ta lalace ne a yankin Owode na Ikorodu Legas lokacin da motar da ta kone ta zo daukar fasinjojin da suka makale.
Kodayake babu fasinjan da ya mutu, wasu sun samu raunuka daban-daban yayin da suke kokarin tserewa.
Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, Mista Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Ya ce, “NEMA, sashin kula da hatsari na 'yan sanda, da ma’aikatan kashe gobara sun ceci fasinjojin ba tare da jin rauni ba. An kawo motar ceto don taimakawa wajen kwashe fasinjojin da suka makale daga motar bas din da ta lalace.
"Motar farko da ke dauke da fasinjojin ta tashi ne daga Ikorodu amma ta lalace a Owode wanda hakan ya sanya bas din da ta kone ta taimaka wa fasinjojin."
KU KARANTA: Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m
A wani labarin, A ci gaba da tashin hankalin da ya ke ta faruwa tsakanin Hausawa da Yarbawa a yankin kudancin Najeriya, wasu 'yan daba suna ta kone-konen motoci da kan manyan hanyoyi.
Daily Trust ta gano hotunan wasu motoci biyu makare da kayan abinci na miliyoyin nairori wadanda ‘yan daba suka cinna wa wuta a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan bayan rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa mazauna ranar Juma’a.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng