Wa’adin Shugaban ‘Yan Sanda zai fuskanci barazana, Lauyoyi sun kai IGP, Buhari kotu

Wa’adin Shugaban ‘Yan Sanda zai fuskanci barazana, Lauyoyi sun kai IGP, Buhari kotu

- Lauyoyin Najeriya sun saba a kan karin wa’adin da aka yi wa Mohammed Adamu

- Shugaban NBA ya ce sam ba za su amince da karin watanni 3 da aka yi wa IGP ba

- Kungiyar ta maka IGP Mohammed Adamu, Shugaban kasa da PSC duk gaban kotu

Kungiyar lauyoyin Najeriya watau NBA ta kai karar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kan kara wa shugaban ‘yan sanda, Mohammed A. Adamu, wa’adi.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kungiyar ta NBA ta shigar da kara ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Fubrairu, 2021, a wani babban kotun tarayya da ke Legas.

A karar mai lamba FHC/L/CS/214/2021, kungiyar ta na tuhumar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sufata-Janar na ‘yan sanda na kasa, da hukumar ‘yan sanda.

NBA ta bukaci kotu ta raba gardama ko shugaban kasa ya na da hurumin da zai kara wa shugaban ‘yan sanda wa’adi bayan ya cika shekarun yin ritaya a aiki.

KU KARANTA: Sufeto na Rundunar ‘Yan Sanda da aka yi a Najeriya a tarihi

A ranar 1 ga watan Fubrairun nan ne IGP Mohammed A. Adamu ya cika shekara 35 ya na aiki a matsayin ‘dan sanda, don haka ya kamata ya yi ritaya a dokar kasa.

Shugaban kungiyar NBA na kasa, Olumide Akpata, ya ce karin wa’adin da aka yi wa Mohammed Adamu ya ci karo da doka, don haka lauyoyi za su kalubalanci batun.

Olumide Akpata ya ce kungiyar NBA ba za ta yi na’am da kowace irin saba doka a Najeriya ba.

“Matakin NBA na daukar wannan matsaya ya zo ne bayan an samu bukatar ayi maza a tsare dokar kasa, a lokacin da ake neman a saba da cin zarafin dokoki.” Inji shi,

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan nada sabon IGP

Wa’adin Shugaban ‘Yan Sanda zai fuskanci barazana, Lauyoyi sun kai IGP, Buhari kotu
Shugaban ‘Yan Sanda na kasa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

NBA ta kai maganar gaban malaman shari’a ne domin su yi fashin-baki. “Matsayar NBA ita ce, “ya kamata Adamu da wasu jami’ai su yi ritaya bayan cika shekara 35 a aiki.”

Akwai yiwuwar cigaba da zaman shugaban ‘Yan Sanda a ofis ya kawo wa gwamnati matsala.

A makon jiya kun ji cewa an samu wani lauya da ya shigar da kara a babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ya na nema a hana Mohammed Adamu aiki a matsayin IGP.

Maxwell Okpara ya shigar da kara ne ya na so a hana Mohammed Adamu shiga ofis saboda ya cika shekarun ritaya, ya kafa hujja da sashe na 215 na kundin tsarin mulki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki.

Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel