Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta magantu a kan nada sabon IGP
- Wa'adin sifeta janar na 'yan sanda, IGP Mohammed Adamu na murabus ya yi a ranar Litinin, kuma har yanzu ba a ji komai ba daga fadar shugaban kasa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bayyana wani lokaci da zai sanar da magajin IGP ba hasali ma mai magana da yawunsa ya ce bai san komai ba a kai
- Duk da dai Garba Shehu ya ce ba za a yi amfani da bangaranci ba idan za a zabi sabon IGP ba kuma cancanta za a duba don tabbatar da kulawa da al'umma
Shiru ake ji dangane da batun zaben sabon Sifeta janar na 'yan sanda sakamakon karewar wa'adin IGP Mohammed Adamu a ranar Litinin.
Fadar shugaban kasa bata sanar da wani tsayayyen lokaci ba na sanar da wanda zai gaji kujerarsa ba, The Nation ta wallafa.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, a ranar Litinin da ana tattaunawa da shi a gidan talabijin din Channels ya ce bai san komai ba dangane da al'amarin.
KU KARANTA: Barawo ya sace sadaki N100,000 daga aljihun waliyyin amarya a masallacin Al Noor
Shehu ya ce ya san dai idan za a sake zaben sabon IGP, cancanta za a duba ba wai bangaranci ba.
"Shugaban kasa zai koma Abuja a ranar Talata. Kuma zai koma bakin aikinsa a ranar Laraba. Ban san lokacin da zai yi magana ba akan wannan al'amarin.
"Abinda zan tabbatar muku shine, Shugaba Buhari zai gwammaci ya samar da sabon sifeta janar wanda zai kula da ni da kai ba wai ya duba kabilanci ba.
"Idan aka duba batun bangaranci kuwa za a iya zaben akalla sifeta janar guda 250, hafsoshin soji guda 250 da sauransu. Don haka ba mai yuwuwa bane," yace.
KU KARANTA: Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno
A wani labari na daban, asbbin hafsoshin tsaron kasar nan sun kai ziyararsu ta farko jihar Borno, jihar da ta kasance filin daga da 'yan Boko Haram.
Sun samu ganawa da Gwamna Zulum a Maiduguri, tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima ya samu halartar zaman.
Shugaban ma'aikatan tsaro, manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugaban sojin tudu, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, shugaban sojin ruwa Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da shugaban sojin sama, Air Vice Marshal isiaka Oladayo Amao zuwa gidan gwamnatin jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng