Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin IGP Adamu da watanni 3, ya bada dalili
- Kamar yadda yayi da hafsoshin tsaro, Buhari ya tsawaita wa'adin IGP na yan sanda
- Ministan harkokin yan sanda ya bayyana dalilin da yasa Buhari yayi hakan
- IGP a Adamu ya cika shekaru 35 a hukumar kuma ya kamata yayi ritaya
Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin Sifeto Janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu, da watanni uku.
Ministan harkokin yan sanda, Mohammad Dingyadi, ya bayyana haka ga manema labaran fadar shugaban kasa ranar Alhamis a Abuja.
Ministan ya bayyana cewa Buhari ya yanke shawara tsawaita wa'adin ne domin bada isasshen lokacin zaben sabon Sifeto Janar.
Za ku tuna cewa tun ranar Litinin ya kamata IGP Adamu yayi ritaya bayan cika shekaru 35 da shiga aikin yan sanda.
Maimakon nada sabon Sifeto da wuri, shugaban kasa bai furta komai kai ba.
KU KARANTA: Olonisakin, Buratai, Ibok-Ete Ibas da Siddique za su zama Jakadu a kasashen waje
DUBA NAN: Boko Haram: Mutanen kananan hukumomin Borno 4 na guduwa zuwa Yobe, Hukumar yan sanda
Wani lauya ya shigar da kara a babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ya na nema a hana Mohammed Adamu aiki a matsayin shugaban ‘yan sanda.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, hakan na zuwa ne bayan Mohammed Adamu ya cika shekarun ritaya daga aiki a ranar 1 ga watan Fubrairu.
Wannan lauya mai suna Maxwell Okpara ya shigar da kara ne a ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairu, 2021, ya na so a hana Mohammed Adamu shiga ofis.
A cewar Maxwell Okpara, tun da Mohammed Adamu ya cika shekara 35 ya na aikin ‘dan sanda, dokar kasa ba ta ba shi damar cigaba da rike mukamin IG ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng