Adamu, da sauran Sufeto na Rundunar ‘Yan Sanda da aka yi a Najeriya

Adamu, da sauran Sufeto na Rundunar ‘Yan Sanda da aka yi a Najeriya

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin Sufeta ‘yan sandan Najeriya, IGP Muhammad A. Adamu.

Mun tattaro maku duka shugabannin ‘yan sandan da aka yi tun bayan lokacin da turawan mallaka su ka mika ragamar aikin ‘yan sanda ga ‘yan kasa.

Louis Edet shi ne mutumin gida da ya fara zama IGP. Kam Salem wanda ya shafe shekaru kusan goma a ofis, shi ne IGP wanda ya fi dade wa a Najeriya.

Ga jerin shugabannin ‘yan sanda na IGP wanda aka yi da kuma shekarun da su ka yi a ofis:

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa su na binciken saba dokar aikin da Kwastam ta yi

1. IGP Louis Edet (1964-1966)

2. IGP Kam Salem (1966-1975)

3. IGP Muhammadu Dikko Yusufu (1975-1979)

Bayan an dawo mulkin farar hula sai Adamu Suleiman ya zama shugaban ‘yan sanda na kasa:

4. IGP Adamu Suleiman (1979–1981)

5. IGP Sunday Adewusi (1981–1983)

6. IGP Etim Inyang (1985–1986)

7. IGP Muhammadu Gambo-Jimeta (1986–1990)

Ibrahim Coomassie wanda ya yi shekaru shida, shi ma ya dade ya na rike da kujerar shugaban ‘yan sanda.

8. IGP Aliyu Atta (1990–1993)

9. IGP Ibrahim Coomassie (1993–1999)

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi alkawari zai ba matasa goyon baya

A cikin shekaru 20 da su ka wuce, an yi shugabannin ‘yan sanda na kasa har goma.

10. IGP Musiliu Smith (1999–2002)

11. IGP Mustafa Adebayo Balogun (2002 – 2005)

12. IGP Sunday Ehindero (2005–2007)

13. IGP Mike Mbama Okiro (2007–2009)

14. IGP Ogbonna Okechukwu Onovo (2009 - 2010)

15. IGP Hafiz Ringim (2010 - 2012)

16. IGP Mohammed Dikko Abubarkar (2012 - 2014)

17. IGP Suleiman Abba (2014 -2015)

18. IGP Solomon E. Arase (2015 - 2016)

19. IGP Ibrahim Kpotun Idris (2016-2019)

20. IGP Mohammed Abubakar Adamu (2019-zuwa yau)

A baya mun kawo maku rahoton manyan attajiran Najeriya 5 masu karancin shekaru a shekarar nan ta 2021 da yadda suka tara dukiyarsu.

Shahararriyar marubuciyar nan Linda Ifeoma Ikeji wanda aka fi sani da Linda Ikeji Linda Ikeji, ita kadai ce mace da ta shigo wannan jeri na fitattun attajirai.

Wannan mace mai shekaru 40 ta mallaki gidan talabijin na Linda Ikeji TV da shafin Linda Ikeji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel