Ritaya: Lauya ya shigar da karar Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya a kotun tarayya

Ritaya: Lauya ya shigar da karar Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya a kotun tarayya

- Maxwell Okpara ya kai karar Shugaban ‘Yan Sanda na kasa a kotun tarayya

- Lauyan ya ce lokaci ya yi da IGP Mohammed Adamu zai tattara ya ajiye aiki

- Wannan Lauya ya hada da Shugaban kasa, AGF da NPC a karar da ya shigar

Wani lauya ya shigar da kara a babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ya na nema a hana Mohammed Adamu aiki a matsayin shugaban ‘yan sanda.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, hakan na zuwa ne bayan Mohammed Adamu ya cika shekarun ritaya daga aiki a ranar 1 ga watan Fubrairu.

Wannan lauya mai suna Maxwell Okpara ya shigar da kara ne a ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairu, 2021, ya na so a hana Mohammed Adamu shiga ofis.

A cewar Maxwell Okpara, tun da Mohammed Adamu ya cika shekara 35 ya na aikin ‘dan sanda, dokar kasa ba ta ba shi damar cigaba da rike mukamin IG ba.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan nadin sabon IGP

Okpara ya nemi Alkali ya tursasa shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumar da ke kula da aikin ‘yan sanda na kasa, su nada sabon magajin IGP Adamu.

Sauran wadanda aka hada a cikin wannan kara su ne; shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Haka zalika wannan lauya ya na karar majalisar NPC mai kula da aikin ‘dan sanda a Najeriya.

A karar da lauyan ya shigar, ya dogara da sashe na 215 na kundin tsarin mulki da bangare na 7 dokar ‘dan sanda, wanda ta tsaida shekarun aikin jami’i a Najeriya.

KU KARANTA: Manyan jami'an 'yan sanda 3 da zasu yi ritaya a Najeriya

Ritaya: Lauya ya shigar da karar Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya a kotun tarayya
IGP Mohammed Adamu Hoto: Twitter @NPF
Asali: Twitter

A cewarsa, daga ranar Litinin bai kamata Mohammed Adamu ya kuma shiga ofis ba, don haka ya bukaci a hana shi yawo da sunan shi ne Sufetan ‘yan sanda na kasa.

A ranar Talata kun ji cewa duk da rade-radin da ke yawo na an maye gurbinsa, IGP Mohammed Adamu ne ya tarbi shugaba Buhari bayan ya iso Abuja daga Daura.

Ana sa ran idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga tafiyar da ya yim zai sanar da sabon sufetan 'yan sanda wanda zai maye gurbin Mohammed Adamu.

Kawo yanzu da ake magana, babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa game da wannan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel